Connect with us

News

‎KANO: Rayuwar Manoma Na Fuskantar Barazana Saboda Hakar Yashi A Madobi ‎

Published

on

IMG 20260101 WA0248 1536x1023
Spread the love

Al’ummar Gobirawa, wani tsohon yankin manoma da ke gabar ruwa a Karamar Hukumar Madobi a Jihar Kano, na fuskantar babbar barazana ga rayuwarsu da hanyoyin samun abinci, sakamakon ci gaba da hakar yashi ba tare da tsari ko kulawar hukuma ba.

Gobirawa na daga cikin tsofaffin yankunan noma a jihar Kano, inda noma ya kasance ginshiƙin rayuwar al’umma tun fiye da shekaru 300 da suka gabata.

APC Gidan Kwankwasiyya Ce Tun Asali” – Waiya Ya Gayyaci Magoya Bayan APC Su Marawa Abba Gida Gaba

Mazauna yankin sun bayyana cewa suna dogaro ne da noman ban-ruwa da na damina, inda ake noma amfanin gona irin su tumatir, barkono, albasa, hatsi, da sauran kayan abinci.

Baya ga haka, yankin na da dumbin itatuwan ‘ya’yan itace kamar mangwaro, lemu, goro, ayaba da cashew, waɗanda ke taimaka wa dubban iyalai wajen samun kuɗaɗen shiga.

Advertisement

Sai dai al’ummar yankin sun ce wannan dogon tarihi na noma na dab da ƙarewa, tun bayan fara hakar yashi kusan shekaru shida da suka gabata.

Wani dattijo manomi a yankin, Malam Nasiru Alasan, ya ce sama da mutane 3,000 a Gobirawa na rayuwa ne kacokan da harkar noma da suka gada daga kakanninsu.

“Fiye da gonaki 100 sun lalace. A duk lokacin damina, ruwa na kwashe sama da mita 30 na ƙasa,” in ji Malam Nasiru.

Wani mazaunin yankin, Malam Jamilu Sulaiman, ya ce matsalar ta fara ne bayan da wani ɗan kasuwa ya fara hakar yashi a Tashar Maza, kusa da gonaki da matsugunan jama’a.

Advertisement

“Ƙasar mu mai albarka tana tafiya da ruwa. Yankin da ya lalace ya zarce kilomita ɗaya, kuma ambaliyar na ƙara matsowa kusa da gidajenmu,” in ji shi.

Ya ce yankunan da matsalar ta fi shafa sun haɗa da Gobirawa, Alwali, Kanawa, Unguwar Mazare, Gidan Bawa, Gangare, Cunkosa da Madobi, tare da wasu sassan Karamar Hukumar Rimin Gado.

A cewarsa, yawancin dankalin Hausa da dankalin Turawa da ake ci a birnin Kano daga waɗannan yankuna ake samar da su.

Masana sun yi gargaɗi kan illar muhalli na dogon lokaci. Dokta Muhammad Yusha’u Gwaram, masanin noma, ya ce zaizayar ƙasa na rage sinadaran da tsirrai ke buƙata, lamarin da ke barazana ga dorewar noma da wadatar abinci.

Advertisement

Ya shawarci gwamnati da al’umma da su ƙarfafa dashe itatuwa da kuma kafa matakan kare muhalli domin rage zaizayar ƙasa.

A nata ɓangaren, Hukumar WECCMA ta ce za ta kai ziyara yankin domin tantance girman barnar tare da ɗaukar matakan da suka dace, ciki har da dakatar da hakar yashi idan ya zama dole.

Al’ummar Gobirawa sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da Karamar Hukumar Madobi da su gaggauta shiga tsakani domin kare gonaki da matsugunan jama’a kafin lokaci ya ƙure.

Ƙoƙarin jin ta bakin wanda ake zargi da hakar yashi a yankin bai yi nasara ba, domin har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a samu amsa daga gare shi ba.

Advertisement

 

 

THE HISTORICA NIGERIA

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *