News
APC Gidan Kwankwasiyya Ce Tun Asali” – Waiya Ya Gayyaci Magoya Bayan APC Su Marawa Abba Gida Gaba
Gwamnatin Jihar Kano ta ce jam’iyyar APC ba baƙuwar gida ba ce ga mabiya tafiyar Kwankwasiyya, tana mai jaddada cewa tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, na daga cikin waɗanda suka assasa jam’iyyar tun farko.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a yayin da yake karɓar mubaya’ar wasu tsofaffin Special Advisers (SAs), Senior Special Assistants (SSAs) da Personal Assistants (PAs) da suka bayyana goyon bayansu ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Waiya ya ce babu wani laifi ko abin mamaki idan gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma jam’iyyar APC, yana mai cewa hakan tamkar komawa gida ne na asali.
“APC gidan duk wani ɗan Kwankwasiyya ce, domin da jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso aka kafa ta. Don haka idan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma APC, to gidan ubansu ya koma, domin su ci gadon da ya dace da su,” in ji Waiya.
Kwamishinan ya ƙara da cewa siyasa tafiya ce ta fahimta da maslahar al’umma, ba wai tsattsauran ra’ayi ba, yana mai kira ga ‘yan siyasa da magoya baya da su fifita zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jihar Kano.
A cewarsa, gwamnatin Abba Kabir Yusuf na maraba da duk wani ɗan siyasa ko jami’i da ke son bayar da gudummawa domin cigaban Kano, ba tare da la’akari da jam’iyyar da ya fito ba.
Tsoffin SAs, SSAs da PAs da suka yi mubaya’ar sun bayyana cewa sun yanke shawarar mara wa gwamnan baya ne bisa abin da suka kira nagartaccen shugabanci da kuma manufofin da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma.
