Connect with us

News

Gwamnan Kano Abba Yusuf Zai Sauya Sheka Zuwa APC A Ranar Litinin 

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, zai shiga jam’iyya mai mulki ta APC a hukumance a ranar Litinin, kamar yadda DAILY NIGERIAN ta rawaito.

Advertisements
Advertisements

Abba Yusuf, wanda shi kaɗai ne gwamna a jam’iyyar NNPP, ya riga ya isa Abuja domin kammala shirye-shiryen sauya shekar tasa.

Advertisements

Akpabio Ya Janye Karar Batanci Da Ya Shigar Kan Natasha

Majiyoyi da ke da masaniya kan shirin sauya shekar gwamnan sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Yitwalda Nentawe, ne za su karɓi gwamnan a Abuja.

Advertisements
Advertisements

Tuni dai an dawo da jagoran APC a Kano, Abdullahi Ganduje, daga wata tafiya da yake yi a Dubai. Haka kuma an umarci shugaban jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas, da ya taƙaita tafiyarsa ta Umara domin ya miƙa katin zama ɗan APC ga gwamnan a mazabarsa ta Diso, da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano, a cikin makon nan.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending