Connect with us

News

Wasu Gungun Ɓata Gari Sun Cinna Wa Wajen Sayar Da Kararen Gurasa Wuta A Rijiya Biyu Da Ke Dala A kano

Published

on

1768950563725

Wasu gungun ɓatagarin da ake zargin ƴan daba ne sun cinna wa wani wurin sayar da karan yin gurasa wuta a unguwar Rijiya Biyu da ke Karamar Hukumar Dala a jihar Kano, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da tashin hankali.

Mazauna yankin sun shaida wa Arewa Update cewa, waɗanda ake zargin sun shigo unguwar ne dauke da makamai, inda suka aikata ɓarna tare da cinna wutar da ta lalata wurin sayar da karan gurasa.

Advertisement

Matsalar Tsaro Da Kuma Lalubo Hanyar Bunkasa Kano Gwamna Abba Kabir Ya Tattauna Da Shugaba Tinubu, Ba Siyasa Ba — Gwamnatin Kano 

Sun ce wannan ba shi ne karo na farko da irin wannan harin ke faruwa ba, domin tun cikin ‘yan kwanakin nan, ɓatagarin ke shigowa yankin lokaci zuwa lokaci suna tayar da hankalin jama’a.

Advertisement

“Sun shigo ranar Lahadi, suka sake dawowa Litinin, sannan ga shi sun dawo Talata,” in ji wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa.

“A wannan karon, sun farfasa wasu gidaje, tare da satar kayayyakin jama’a.”

Advertisement

Rahotanni daga yankin sun nuna cewa, sakamakon hare-haren, wasu mazauna unguwar sun fara ficewa daga gidajensu domin gudun kar tashin hankalin ya shafi rayukansu da dukiyoyinsu.

Wasu maƙota sun ce suna rayuwa cikin fargaba, musamman da daddare, inda suka ce ba su samun isasshen barci saboda tsoron afkawar ƴan daban a kowane lokaci.

Advertisement

Al’ummar yankin sun yi kira ga rundunar ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar mataki domin dakile wannan ɗabi’a, tare da tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda ta jihar Kano dangane da lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending