Connect with us

News

gwamnan sokoto ya bayar da umarnin Biyan Ma’aikata Albashi Saboda Azumi

Published

on

Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya bayar da umarnin biyan ma’aikatan jihar albashin watan Fabarairu nan take, saboda ƙaratowar watan azumin Ramadana.

Aliyu ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa ta hannun shugaban sashen yada labarai da hulɗa da jama’a na ofishin gwamnan, Abubakar Bawa a yau Alhamis.

Hukumar FRSC Ta Sallami Jami’anta  43 Daga Aiki Sakamakon Laifuffukan Da Suka Aikata

Sanarwar ta ce matakin ya shafi: “ma’aikatan Gwamnatin jiha, ƙananan hukumomi, ma’aikatan hukumar Ilimi ta ƙananan hukumomi, da kuma tsofaffin ma’aikata masu karɓar fansho a faɗin jihar”.

Bayanin ya ƙara da cewa matakin fara biyan albashin zai fara aiki ne daga ranar Juma’a 13 ga watan na Fabarairu kamar yanda BBC ta ruwaito

A ranar 18 ko 19 ga watan Fabarairun nan ne ake sa ran al’ummar Musulumi na duniya za su fara azumin watan Ramadana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending