Connect with us

News

Hukumar FRSC Ta Sallami Jami’anta  43 Daga Aiki Sakamakon Laifuffukan Da Suka Aikata

Published

on

Hukumar Kiyaye Haddura ta Nijeriya (FRSC) ta sallami jami’ai 43 daga aiki sakamakon laifuffukan da suka aikata.

Jami’an da abin ya shafa sun hada da 31 da aka kora saboda barin wurin aiki ba tare da izini ba, biyar saboda halaye marasa kyau, da kuma bakwai saboda rashin ƙwarewa da saba ƙa’ida yayin aikin sintiri.

Advertisement

Malam Nasir El-Rufai Zai Bayyana A Gaban EFCC Ranar Litinin

Hukumar ta bayyana cewa wannan mataki sakon gargadi ne cewa tambarin hukumar ta FRSC alama ce ta mutunci da alhaki mai nauyi.

Advertisement

“Duk wani jami’i da ya zabi karya ka’idojin wannan cibiyar mai daraja zai fuskanci cikakken hukuncin ladabtarwa na hukumar.” in ji hukumar.

Babban Kwamandan FRSC, Mallam Shehu Mohammed, yayin da yake magana kan lamarin a Abuja, ya bayyana matakin a matsayin tabbaci mai karfi na manufar hukumar ta lamuncewa da rashin ɗa’a da karya ka’idojin aiki.

Advertisement

Mallam Mohammed ya jaddada cewa FRSC a matsayin mai bin tsauraran ƙa’idojin aiki, ba za ta amince da duk wani lamari da zai jawo rashin aminci tsakaninsu da jama’a ko taɓa mutuncin hukumar ko cikas ga ayyukanta.

A cewarsa, barin aiki ba tare da izini ba karya doka ce babba, da kuma saɓa rantsuwar aiki, musamman a hukuma mai alhakin kare rayukan miliyoyin masu amfani da hanyoyi a kullum

Advertisement

Ya kara da cewa halaye marasa kyau da rashin ƙwarewa yayin sintiri na rage amincewar jama’a tare da saba wa manyan ƙa’idojin hukumar na ladabi, gaskiya da kwarewar aiki.

Ya ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewa hukumar FRSC za ta kara sa ido a cikin gida, ta hanyar ƙarfafa tsarin kulawa, tare da inganta koyar da ɗabi’u masu kyau a dukkan rundunoninta a fadin kasa.

Advertisement

Mallam Mohammed ya kuma bukaci masu ababen hawa su ci gaba da yarda da FRSC tare da tallafa wa kokarinta na tabbatar da hanyoyi masu aminci ga kowa.

 

Advertisement

 

TRT AFRIKA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending