News
Jami’an ’Yansanda Sun Dakatar Da Wasan Tashe A Kano
Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sanar da dakatar da wasan gargajiya na Tashe a duk faɗin jihar a wannan watan na Ramadan, saboda dalilan tsaro.
Hukumar ta ce an ɗauki matakin ne tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar domin hana masu aikata laifi amfani da tarukan Tashe wajen aikata miyagun ayyuka, ciki har da daba, ƙwacen waya da kuma shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
Falalar Kwanaki 10 Na Tsakiyar Watan Ramadan
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa rundunar ta tanadi matakan tsaro domin tabbatar da an gudanar da azumin cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya kuma buƙaci iyaye da masu kula da yara su ƙara sa ido, tare da gargadin matasa kan shiga duk wani taro da ka iya haddasa tashin hankali ko karya doka.
A cewarsa, duk wanda aka samu da laifin karya doka zai fuskanci hukunci mai tsanani.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya buƙaci jama’a su riƙa kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba ta lambobin waya:
08032419754, 08123821575, 08076091271, 09029292926,
ko kuma ta manhajar NPF Rescue Me da ake samu a Play Store.
Rundunar ta jaddada cewa haɗin kan al’umma da hukumomin tsaro na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya a duk tsawon watan Ramadan.
