Connect with us

News

Shugaba Tinubu ya sake naɗa Abubakar Audi a Kwamanda Janar Na NSCDC

Published

on

NSCDC CG Ahmed Abubakar Audi

Shugaba Bola Tinubu ya sake naɗa Dakta Ahmed Abubakar Audi a matsayin Kwamanda-Janar na Hukumar Tsaron al’umma ta Cibil Defense (NSCDC) na wani sabon wa’adin shekaru biyar.

Sabon naɗin ya fara aiki ne q ranar Juma’a, 27 ga Fabrairu, 2026 .

Advertisement

An fara naɗa Dakta Audi a wannan matsayi ne a shekarar 2021 ta hannun tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Wa’adinsa na farko na shekaru biyar ya ƙare ne a ranar Juma’ar da ta gabata yayin da yake halartar bikin Ranar Kariya ta Duniya ta 2026 a hedikwatar NSCDC ta ƙasa da ke Abuja.

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Masu Safarar Makamai A Kaduna

Advertisement

Litinin mai zuwa ake sa ran Audi zai koma bakin aikinsa ranar tare da sabon ƙuduri da sabon wa’adi.

Shugaba Tinubu ya umarci Audi da ya sake fasalta da inganta hukumar domin ta taka muhimmiyar rawa a harkokin tsaron ƙasa, musamman a lokacin da rundunar ’yan sanda ke mai da hankali kan babban aikinta na kare ’yan ƙasa daga ’yan fashi da makami, masu garkuwa da mutane da ’yan ta’adda.

Advertisement

An haifi Dakta Audi a ranar 30 ga Satumba, 1967 a garin Laminga, Ƙaramar Hukumar Nasarawa, Jihar Nasarawa. Bayan ya kammala karatunsa na farko a jihar, ya halarci Kwalejin Horar da Malamai ta Jengre a Jihar Plateau, inda ya samu takardar shaidar Teachers’ Grade II a shekarar 1987.

Daga nan ya wuce Kwalejin Ilimi ta Akwanga, inda ya samu takardar shaidar NCE a shekarar 1992. Saboda ƙwazon neman ilimi, ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya kammala digirinsa na farko a fannin Ilimin Jiki da Lafiya (Physical and Health Education) a shekarar 1995.

Advertisement

A shekarar 2001 ya samu digiri na biyu (Masters) a fannin Gudanar da Harkokin Mulki (Public Administration) daga Jami’ar Calabar. A shekarar 2014 ya samu digirin digirgir (PhD) a fannin Public Administration daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, sannan a shekarar 2019 ya sake samun digiri na biyu a fannin Law Enforcement and Criminal Justice (MLCJ) daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Dakta Audi ya shiga NSCDC a watan Nuwamba 1996 a matsayin mai aikin sa kai, sannan aka tura shi a matsayin Jami’in Rukuni (Divisional Officer) a ƙaramar hukumar Obi, Jihar Nasarawa, bayan ya kammala horon jami’ai a shekarar 1997.

Advertisement

Ya yi aiki a sassan jihohi daban-daban, kuma a shekarar 2007 aka ɗaga shi zuwa mukamin Commandant na Hukumar, daga bisani aka tura shi ofishin Kwamanda-Janar a Hedikwatar Ƙasa da ke Abuja.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending