Connect with us

News

Jami’an NSCDC Sun Kama Matasa 4 Yayin Da Suka Fito Kwacen Wayoyin Masu Zuwa Tahajjud A Kano 

Published

on

IMG 20260313 WA0008

Jami’an Tsaron Civil Defence a Jihar Kano sun kama wasu matasa hudu da ake zargi da tayar da tarzoma da kuma kwacen waya lokacin sallar Tahajjud a unguwar Dorayi Babba da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano.

Wannan na kunshe ne ta cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar a Kano SC Ibrahim Idris Abdullahi ya fitar a ranar Jumuʼa 13 ga Maris 2026.

Advertisement

Takaddamar Nukiliyar Iran Da Yammacin Duniya/Amurka Da Isra’ila: Za A Iya Samun Mafita?

Sanarwar ta ce jami’an hukumar sun kama matasan ne yayin sintiri bayan samun bayanin cewa wasu gungun matasa dauke da makamai suna kai hari ga masu gudanar da sallar Tarawihi da kuma masu wucewa a kusa da wata makaranta da ke Dorayi Babba.

Advertisement

Sanarwar ta ce jami’an sun fatattaki matasan tare da kama wasu daga cikinsu bayan sun kai hari ga wani mutum tare da kwace masa wayarsa.

Sanarwar ta kara da cewa bincike kan lamarin ya kammala kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending