News
Shugaba Tinubu Ya Kafa Kwamitin Gyara Harkar Man Fetur A Najeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa wani kwamiti na musamman domin ɓullo da sabbin matakan gyare-gyare a ɓangaren harkar man fetur a Najeriya.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Jami’an NSCDC Sun Kama Matasa 4 Yayin Da Suka Fito Kwacen Wayoyin Masu Zuwa Tahajjud A Kano
A cewar sanarwar, Fola Adeola, wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa bankin Guaranty Trust Bank kuma shugaban Fate Foundation, shi ne zai jagoranci kwamitin.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Ademola Adeyemi-Bero, Osagie Okunbor, Abubakar Suleiman, Adaeze Aguele, Farouk Gumel, Phillipa Osakwe-Okoye da Seyi Bella, yayin da Mofoluwasho Fadayomi zai zama sakataren kwamitin.
An ɗora wa kwamitin alhakin tsara matakan gyare-gyare da za su bunƙasa harkar man fetur, su jawo ƙarin zuba jari, tare da ƙara wa tattalin arziƙin ƙasar nan daraja.
Kwamitin zai riƙa kai rahoto kai-tsaye ga shugaban ƙasa duk wata, sannan zai gabatar da rahoton wucin gadi bayan watanni uku, yayin da ake sa ran kammala rahoton ƙarshe cikin watanni shida.
Ana sa ran kwamitin zai gabatar da manyan tsare-tsare uku na gyara, ciki har da matakan sauya tsarin ɓangaren nan take.
Shirin zai bayar da damar samun jarin dala biliyan biyar zuwa 10, da kuma wani tsari na sauya tsarin makamashi na ƙasa na tsawon shekaru 10.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News5 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News4 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
