News
Ambaliyar Ruwa Ta Yi Ajalin Sama Da Mutane 100 Iyalai 2,700 Sun Rasa Muhallansu A Kenya
Ambaliyar ruwa mai tsanani ta kashe akalla mutane 108 tare da raba iyalai sama da 2,700 da matsugunansu a sassa daban-daban na ƙasar Kenya, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.
Hukumar ’yan sandan ƙasar ta ce ambaliyar ta biyo bayan mamakon ruwan sama da aka shafe makonni ana yi, wanda ya haddasa mummunar ɓarna ga rayuka da dukiyoyi.
“Rashin Bai Wa Yara Cikakkiyar Kula Na Haifar Da Matsala A Rayuwarsu” —Dokta Hadiza
Rahotanni sun nuna cewa ambaliyar gaggawa da ta fara a daren 6 ga watan Maris ta lalata kadarori da dama, ciki har da motoci, tare da katse zirga-zirgar jiragen sama da kuma wutar lantarki a wasu yankuna.
Dubban mazauna yankunan da abin ya shafa sun tsere daga gidajensu domin tsira da rayukansu, yayin da hukumomi ke ci gaba da ƙoƙarin kai agaji ga waɗanda abin ya rutsa da su.
Ko da yake ruwan sama ya ragu a wasu wurare, jami’an tsaro sun gargadi jama’a da su guji zama a yankunan da ke cikin haɗari, suna mai cewa barazanar ambaliya na nan daram, musamman sakamakon toshewar magudanan ruwa da ƙasa da ta jike.
Masana na ganin cewa wannan bala’i ya sake fito da buƙatar ɗaukar matakan gaggawa da na dogon lokaci domin rage tasirin ambaliya a ƙasar.
