News
“Rashin Bai Wa Yara Cikakkiyar Kula Na Haifar Da Matsala A Rayuwarsu” —Dokta Hadiza
Shugabar makarantar Intercontinental Schools, Dokta Hadiza N. Yusuf Baba, ta yi gargadi kan illar da rashin bai wa yara cikakkiyar kulawa ke haifarwa, tana mai cewa hakan na jefa su cikin matsaloli masu yawa a rayuwa.
Doktar ta bayyana haka ne yayin wata tattaunawa Muhasa TV/Radio ,inda ta ce kulawar iyaye da al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen gina halayen yara tun daga ƙuruciya.
Mawakin Gambara Ya Zama Sabon Firaminista A Nepal
A cewarta, yara da ba sa samun kulawa ta gari kan fuskanci matsaloli kamar tabarbarewar tarbiyya, rashin mayar da hankali a karatu da kuma fadawa cikin halaye marasa kyau.
“Rashin kulawa daga iyaye da masu kula da yara na iya jefa su cikin matsaloli masu tsanani da za su iya shafar makomarsu,” in ji ta.
Dokta Hadiza ta ƙara da cewa duk da irin rawar da makarantu ke takawa wajen koyarwa da tarbiyya, har yanzu iyaye ne ke da babbar rawa wajen tsara makomar ‘ya’yansu.
Ta kuma yi kira ga iyaye da su ƙara himma wajen ba ‘ya’yansu kulawa ta musamman, tare da kula da iliminsu da halayensu domin tabbatar da samun kyakkyawar makoma.
A ƙarshe, ta buƙaci gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wa shirye-shiryen inganta rayuwar yara, domin samar da al’umma mai inganci a nan gaba.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
