Connect with us

News

Indonesiya Ta Haramtawa Yara Yan Kasa Da Shekaru 16 Amfani Da Social Media

Published

on

1774749850140

Gwamnatin ƙasar Indonesia ta sanar da haramta wa yara ‘yan ƙasa da shekaru 16 amfani da kafafen sada zumunta, a wani mataki da ta ce na da nufin kare lafiyar kwakwalwa da tarbiyyar matasa.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan sabuwar doka ta shafi shahararrun manhajoji irin su Facebook, Instagram, da TikTok, inda za a hana yara ƙanana bude asusu ko amfani da su ba tare da kulawar iyaye ba.

Mawakin Gambara Ya Zama Sabon Firaminista A Nepal

Mahukuntan ƙasar sun bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne sakamakon karuwar matsalolin da suka shafi shaye-shayen intanet, rashin barci, da kuma tasirin da ke illa ga halayyar yara. Sun kuma jaddada cewa doka na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi wajen inganta tsaron yara a duniyar zamani.

A cewar jami’an gwamnati, kamfanonin da ke kula da wadannan manhajoji za su dauki alhakin tabbatar da bin sabuwar dokar, tare da kafa hanyoyin tantance shekaru da kuma kariya ga masu amfani da su.

Sai dai wasu masu rajin kare hakkin dan Adam sun nuna damuwa kan yadda dokar za ta iya takaita ‘yancin yara wajen samun bayanai da mu’amala da duniya, suna masu kira da a tabbatar da an aiwatar da ita cikin adalci da tsari.

Advertisement

Masana sun ce matakin na Indonesia na iya zama abin koyi ga sauran kasashe da ke fuskantar irin wadannan kalubale, musamman wajen daidaita amfani da fasaha da kare tarbiyyar al’umma.

 

DW

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending