Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Umarci Kamfanonin Waya Su Biya Mutane Diyya Saboda Karancin Network

Published

on

images

Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta umarci kamfanonin sadarwa da su biya diyya ga masu amfani da layukansu a yankunan da ake fama da matsalar ƙarancin ingancin sabis.

A cikin wata sanarwa da shugabar sashen hulɗa da jama’a ta hukumar, Nnenna Ukoha ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa za a bai wa waɗanda matsalar ta shafa katin kiran waya (airtime), gwargwadon yadda suke kashe kuɗi da kuma yankunan ƙananan hukumomin da matsalar ta fi kamari.

Advertisement

Kwankwaso Ya Sanar Da Ficewar Sa Daga Jam’iyyar NNPP

Hukumar ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinta na kare haƙƙin masu amfani da harkar sadarwa a ƙasar, tare da jaddada cewa bai dace a ɗora wa masu amfani da layukan waya cikakken nauyin matsalolin da ke faruwa sakamakon gazawar kamfanoni wajen cika ƙa’idojin aiki ba.

Advertisement

NCC ta kuma umarci kamfanonin hasumiyar sadarwa da su inganta kayayyakin aiki da cibiyoyin sadarwa, domin tabbatar da ingantaccen sabis ga al’umma.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da masu amfani da layukan waya a sassa daban-daban na ƙasar ke ci gaba da korafin yawan katsewar kira da kuma matsalolin sadarwa, wanda ke shafar harkokin kasuwanci da mu’amalolin yau da kullum.

Advertisement

 

KANO TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending