Connect with us

News

Kano: Ɗaya Daga Cikin Jarirai Biyar Ta Rasu, Huɗu Na Ci Gaba Da Karɓar Kulawa A ICU

Published

on

FB IMG 1774817803009 768x420

Kano: Ɗaya Daga Cikin Jarirai Biyar Ta Rasu, Huɗu Na Ci Gaba Da Karɓar Kulawa A ICU

Ɗaya daga cikin jarirai biyar da aka haifa a Jihar Kano ta rasu, yayin da sauran huɗu ke ci gaba da karɓar kulawa ta musamman a asibiti, bayan haihuwarsu kafin cikar lokaci.

Advertisement

Jami’an asibitin sun tabbatar da rasuwar jaririyar a ranar Lahadi, sakamakon matsalar numfashi (apnoea) da ta janyo tabarbarewar lafiyarta, duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi na ceton rayuwarta ta hanyar ƙarin jini. Rahotanni sun nuna cewa jaririyar na da nauyin kilo 1.3 a lokacin rasuwarta.

Zazzabin Lassa: Mutum 146 Sun Mutu, Jami’an Lafiya 38 Sun Kamu  — Gwamnatin Tarayya 

Advertisement

‎Sauran jarirai huɗun na cikin mawuyacin hali, inda ake kula da su a sashen kulawa ta musamman ga marasa lafiya masu tsananin buƙata.

‎Mai magana da yawun Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano, Samira Suleiman, ta bayyana cewa an haifi jariran ne ba su kai cikakken lokacin haihuwa ba, lamarin da ya sa aka garzaya da su kai tsaye zuwa sashen kulawa ta musamman domin ceton rayukansu.

Advertisement

‎Ta ce ana kula da su ne saboda ƙarancin nauyin jikinsu da kuma haɗarin kamuwa da cututtuka, ciki har da kamuwa da ƙwayoyin cuta, rawayar jiki (jaundice), da kuma matsalolin daidaita zafin jiki da sukari a jini.

‎A wani ɓangare mai tayar da hankali kuwa, rahotanni sun nuna cewa mahaifiyar jariran ta rasu a daren Laraba sakamakon zubar jini mai tsanani bayan haihuwa.

Advertisement

 

 

Advertisement

KANO FOCUS

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending