Connect with us

News

Zazzabin Lassa: Mutum 146 Sun Mutu, Jami’an Lafiya 38 Sun Kamu  — Gwamnatin Tarayya 

Published

on

Zazzabin Lassa Cutar ta yi Ajalin Mutum 118 A Cikin Watanni Uku

Gwamnatin Tarayya ta ce akalla mutum 146 ne suka mutu sakamakon cutar zazzabin Lassa daga watan Janairu zuwa tsakiyar Maris na shekarar 2026.

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta bayyana hakan ne a cikin rahoton mako na 11 na yaduwar cutar da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, wanda ya kunshi bayanai daga ranar 9 zuwa 15 ga watan Maris.

Advertisement

An Sanya Dokar Hana Fita Ta Sa’o’i 48 A Jos ‎

A cewar hukumar, adadin mace-macen ya kai kashi 25.1 cikin dari a bana, wanda ya fi na shekarar 2025 da ya tsaya a kashi 18.7 cikin dari.

Advertisement

NCDC ta ce yawan masu kamuwa da cutar ya karu daga mutum 40 a mako na 10 zuwa mutum 66 a mako na 11, lamarin da ke nuna yadda cutar ke kara yaduwa a wasu sassan kasar.

Rahoton ya nuna cewa an samu karin yaduwar cutar ne a jihohin Taraba, Filato, Edo, Benuwe, Kogi, Gombe da Neja.

Advertisement

Hukumar ta kara da cewa zuwa yanzu an samu bullar cutar a kananan hukumomi 82 da ke cikin jihohi 21 a fadin kasar.

Sai dai jihohin Bauchi, Ondo, Taraba, Benuwe da Edo ne ke dauke da kaso mafi yawa na masu dauke da cutar, inda suka kai kashi 85 cikin dari na jimillar wadanda suka kamu a shekarar 2026.

Advertisement

Game da masu kamuwa da cutar, NCDC ta ce mutane masu shekaru tsakanin 21 zuwa 30 ne suka fi kamuwa, duk da cewa an samu masu dauke da cutar daga shekara 1 zuwa 90.

A bangaren jami’an lafiya kuwa, hukumar ta ce mutum 38 ne suka kamu da cutar a bana, abin da ke nuna irin barazanar da ma’aikatan lafiya ke fuskanta.

Advertisement

Sai dai hukumar ta ce ba a samu karin jami’an lafiya da suka kamu da cutar ba a cikin mako na 11.

NCDC ta danganta kamuwar jami’an lafiya da cutar da dalilai kamar rashin amfani da kayan kariya yadda ya kamata, jinkirin gano cutar, da kuma gazawar wasu cibiyoyin lafiya wajen daukar matakan kariya.

Advertisement

Hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da daukar matakan dakile yaduwar cutar tare da karfafa wayar da kan jama’a.

Ta kuma yi kira ga al’umma da su rika garzayawa asibiti da zarar sun fara jin alamun rashin lafiya, tare da gujewa yin magani a gida, tana mai cewa hakan na kara yada cutar da kuma janyo asarar rayuka.

Advertisement

 

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending