News
Shugaba Tinubu Na Son Majalisar Dokoki Ta Amince A Kara Naira Tiriliyan 9 A Kasafin Kudin 2026
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya rubuta wasiƙa zuwa Majalisar Dokoki ta Ƙasa yana neman a yi gyara a kan Kudirin Kasafin Kuɗi na shekarar 2026, inda ya ba da shawarar ƙara naira tiriliyan 9 domin a mayar da jimillar kasafin daga naira tiriliyan 58.4 zuwa naira tiriliyan 67.4.
An isar da wannan buƙata ne ta cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya karanta a zauren majalisar yayin zamanta na ranar Talata.
Mahara sun kai sabon hari a kauyen da suka kashe masu bikin aure a Kaduna
A cewar Shugaban Ƙasar, wannan gyara da ake so an yi shi ne domin ƙarfafa gaskiya a harkokin kuɗi da kuma tabbatar da aiwatar da manyan shirye-shiryen ƙasa yadda ya kamata.
Ya bayyana manyan manufofi uku da ke bayan wannan buƙata, ciki har da daidaita tare da yin bayanin duk wasu basussukan doka da suka rage daga kasafin kuɗin da suka gabata, domin kauce wa su zama nauyi ga aiwatar da kasafin shekarar 2026.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
