News
INEC Dakatar Da Aikin Sake Tantance Rajistar Masu Zaɓe Har Zuwa Bayan Babban Zaɓen 2027
Hukumar INEC mai shirya zaɓe a Najeriya ta sanar da dakatar da aikin sake tantance rajistar masu zaɓe har zuwa bayan zaɓen 2027 da ke tafe a shekara mai zuwa.
Wannan mataki ya biyo bayan tattaunawa da aka yiyi tsakanin masu ruwa da tsaki da kuma ƙusoshin hukumar.
SOKOTO: Hare-haren Ƴan Ta’adda Sun Tilasta Mazauna Ƙauyuka 21 Tserewa Daga Gidajensu
Tantance rajistar masu zaɓe na zama ɗaya daga cikin muhimman ayyukan hukumar, na tabbatar da sahihin zaɓe da kuma baiwa marasa rajistar zaɓe yin tasu rajistar don samun damar kaɗa ƙuri’a.
A yayin wannan aiki, akan tabbatar da suna da sauran bayanan mamallakin katin zaɓe da kuma yin duk wasu gyare-gyare idan an sami kuskure.
A cikin sanarwar da INEC ta fitar ta kuma jadaddawa ƴan ƙasar cewa tana kan bakanta na tabbatar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe da zai zama abin kwatance a Najeriya dama idanun duniya.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
