Connect with us

News

Gwamnan Kano Ya Ce Mataimakinsa Ya Yi Ƙula-Ƙula Domin Ganin Ya Hamɓarar Da Shi Daga Kan Mulki

Published

on

GMVX6dqWoAAIJRF (1)

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa tsohon mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi ƙoƙarin kifar da shi daga mulki domin ya karɓi ragamar mulkin jihar.

Gwamnan, ya yi wannan zargin ne yayin da ya karɓi baƙuncin wasu mawaƙa a Fadar Gwamnati da ke Kano a ranar Alhamis.

Advertisement

INEC Dakatar Da Aikin Sake Tantance Rajistar Masu Zaɓe Har Zuwa Bayan Babban Zaɓen 2027

An ruwaito cewa Gwarzo ya yi murabus daga muƙaminsa ne a daidai lokacin da Majalisar Dokokin Jihar Kano ke shirin tsige shi.

Advertisement

Sai dai daga baya majalisar ta janye shirin tsige shi bayan ya riga ya sauka daga muƙamin da kansa.

Yayin da yake yi wa mawaƙan jawabi, Gwamna Abba, ya bayyana cewa shi ma bai ga takardar murabus ɗin tsohon mataimakin nasa ba.

Advertisement

Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ba ta yi masa wani laifi ba.

“Yau ga shi mataimakin gwamnan da muka zo tare a tikiti ɗaya ba ya tare da mu. Babu wanda ya ɓata masa rai. A gaskiya, ban ma ga takardar murabus ɗinsa ba, me ya shafe ni da ita?” in ji shi.

Advertisement

“Duk abin da ya sa ya yi hakan, ƙoƙari ne na maye gurbina domin ya karɓi kujerar, amma Allah bai yarda ba,” in ji Abba.

Gwamnan, ya kuma nuna damuwarsa kan yadda aka gudanar da al’amura game da tsohon mataimakin a cikin tafiyar Kwankwasiyya, inda ya tambayi dalilin da ya sa ba a ba shi damar da yake nema ba tun farko.

Advertisement

“Mataimakin gwamnan da ya tafi yana fatan samun wannan tikiti (na gwamna), me ya yi ba daidai ba? Me ya sa ba a ba shi tikitin ba? Wannan ba cin amanarsa aka yi ba?”

A bayyane yake su wane ne maciya amana na gaskiya

Advertisement

Gwamnan ya kuma mayar da martani ga masu sukar matakin da ya ɗauka na sauya sheƙa, cewa abubuwan da ke faruwa sun nuna su wane ne “maciya amana” da kuma “abokan gaba” a cikin tafiyar siyasarsu.

Idan ba a manta ba a baya, gwamnan ya fice daga jam’iyyar NNPP.

Advertisement

Ya bayyana cewa wannan mataki da ya ɗauka domin amfanin al’ummar Kano ne, ba wai cin amana ba kamar yadda wasu ke zargi.

Ya ƙara da cewa waɗanda ke zarginsa da cin amana, su ma sun taɓa ɗaukar irin wannan matakin a baya, sai dai yanzu sun manta da hakan.

Advertisement

“’Yan Kwankwasiyya ba a ma sanar da su ba kafin a yanke shawarar ficewa daga NNPP, to su ma an ci amanarsu ko ba a ci ba?” ya tambaya.

Abba ya ce matakin nasa ya taimaka wajen kauce wa jefa al’ummar Kano cikin ruɗani.

Advertisement

Ya ƙara da cewa dukkanin ƙoƙarin da suka yi na gyara matsalolin cikin gida na jam’iyyar, an yi watsi da su.

“Mun hango inda jam’iyyar ta dosa, muka ba da shawara amma aka yi watsi da ita. Allah Ya nuna mana hanya, muka fita saboda ba ma son jefa miliyoyin al’ummar Kano cikin ruɗani,” in ji shi.

Advertisement

Ya ƙara da cewa abubuwan da ke faruwa yanzu sun tabbatar da duk abin da ya faɗa tun kafin ya fice daga jam’iyyar.

Gwamnan ya kuma soki yadda ake fifita sabbin ’yan siyasar da suka sauya sheƙa, duk da cewa a baya sun kasance masu adawa da tafiyar tasu.

Advertisement

“Yanzu wanda a da shi ne babban abokin gabanmu kuma ya jefa mu cikin ƙalubale a lokacin zaɓe, shi ne a yanzu ake son ba shi tikiti. Wannan ba cin amanar ’yan Kwankwasiyya ba ne?” ya tambaya.

Gwamna Abba, ya jaddada cewa gwamnatinsa na ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, yana mai cewa mutane masu nagarta sun riga sun fara nuna sha’awar cike gurbin mataimakin gwamna.

Advertisement

“Za mu ci gaba da zama a nan har zuwa ranar da Allah Ya ƙaddara mu bar mulki. Muna godiya a gare Shi. Yanzu mataimakin gwamna ya tafi, kuma mutane na gari suna neman wannan muƙami,” in ji shi.

Daga ƙarshe, ya sake taɓo batun wasu tsare-tsaren siyasa da ke gudana, musamman fifita sabbin mambobi a kan tsofaffin mambobin jam’iyya.

Advertisement

“Yau wanda shi ne babban abokin gaban Kwankwasiyya shi ne ake shirin bai wa tikitin takarar gwamna. Bai daɗe da shiga ba, amma ana rainonsa domin wannan muƙami. Wannan ba cin amanar ’yan Kwankwasiyya ba ne?

 

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending