Connect with us

News

IGP Disu Ya Kafa Sabuwar Rundunar Musamman Don Yaƙi Da Manyan Laifuka

Published

on

Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Olatunji Disu, a ranar Talata ya kira wani taron gaggawa da manyan shugabannin rundunar ‘yan sandan Najeriya, inda ya sanar da manyan sauye-sauyen aiki, ciki har da kafa sabuwar runduna ta musamman domin yaƙi da manyan laifuka a faɗin ƙasar.

A cewar wata sanarwa da kakakin ‘yan sanda, Anthony Placid, ya fitar, taron wanda aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Abuja, ya haɗa da mambobin tawagar gudanarwa, Mataimakan Sufeto Janar (AIGs) da Kwamishinonin ‘Yan Sanda domin tattauna matsalolin tsaro da ƙarfafa bin doka da oda a dukkan rundunoni.

Advertisement

Karon Farko Cikin Shekaru 20, Arsenal Ta Kai Wasan Ƙarshe A Champions League

Babban abin da ya fito fili daga cikin sauye-sauyen shi ne kafa rundunar (Violent Crime Response Unit (VCRU), wata sabuwar runduna da aka sake fasalinta domin ƙarfafa martani cikin gaggawa ga manyan laifuka. Disu ya ce rundunar za ta yi aiki ne bisa sahihan bayanan sirri, tare da horo na musamman, mutunta haƙƙin ɗan Adam, da kuma tsauraran matakan kula da aiki, inda Kwamishinonin ‘Yan Sanda za su riƙa da alhakin sa ido kai tsaye.

Advertisement

Ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin yunƙurin sauya tsarin aikin ‘yan sanda zuwa wanda ya fi tsari, gaskiya da kuma amfani da bayanan sirri, domin fuskantar sabbin ƙalubalen tsaro a ƙasar.

Nasarorin ayyuka

Advertisement

IGP ɗin ya kuma bayyana manyan nasarorin da rundunar ta samu a watan Afrilu, yana mai cewa amfani da bayanan sirri ya taimaka matuƙa wajen cimma waɗannan nasarori.

A cewarsa, an kama mutum 28 da ake zargi da ta’addanci, 85 da ake zargi da garkuwa da mutane, 62 da ake zargi da fashi da makami, 51 da ake zargi da kisan kai, da kuma 54 da ake zargi da shiga ƙungiyoyin asiri.

Advertisement

Haka kuma, an ceto mutum 189 da aka yi garkuwa da su, yayin da aka kwato bindigogi 140, harsasai 1,074 da kuma motoci 37 da aka sace.

Ƙarfafa hulɗa da al’umma

Advertisement

Mista Disu ya kuma umarci Kwamishinonin ‘Yan Sanda a duk faɗin ƙasa da su ƙarfafa tsarin hulɗa da al’umma ta hanyar shirya tarukan tattaunawa da sarakuna, malamai da sauran masu ruwa da tsaki.

Haka kuma ya umarci shugabannin ‘yan sanda a jihohi da su sanya lambobin wayarsu a fili domin ƙarfafa amincewar jama’a da kuma sauƙaƙa sadarwa.

Advertisement

Kisan Delta: An sallami jami’ai, za a gurfanar da su

IGP ɗin ya kuma yi tsokaci kan kisan da aka yi wa wani wanda ake zargi a Jihar Delta ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa hakan ya saɓa da dokokin rundunar.

Advertisement

Ya tabbatar da cewa an kori jami’an da abin ya shafa daga aiki, kuma an miƙa lamarin domin a gurfanar da su a gaban kotu.

Disu ya jaddada cewa rundunar na da manufar rashin jurewa duk wani rashin ɗa’a, yana mai cewa babu wani jami’i da ya fi ƙarfin doka.

Advertisement

Ya ƙara da cewa dukkan sauye-sauyen da ake yi a rundunar sun dogara ne kan ƙwarewa, ladabi da mutunta haƙƙin ɗan Adam, tare da amfani da hanyoyin tabbatar da gaskiya kamar sashen karɓar ƙorafe-ƙorafe na ‘yan sanda (CRU).

 

Advertisement

 

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending