News
Gwamnatin Tarrayya Ta Haramta Sanya ‘Dr’ Ga Sunayen Wadanda Aka Ba Digirin Girmamawa
Gwamnatin Tarayya ta hana duk wanda aka ba digirin girmamawa amfani da lakabin “Dr” a sunansa. Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Ya ce an ɗauki matakin ne a zaman majalisar zartarwa ta ƙasa da aka gudanar ranar 30 ga Afrilu, domin dakile yadda ake bai wa mutane digirin girmamawa ba bisa ƙa’ida ba, musamman don siyasa da neman kuɗi. Ya kuma ce bayar da irin waɗannan digiri ga masu rike da muƙaman gwamnati ya saɓa da ƙa’idojin da suka dace.
Bichi Ya Ayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Sanatan Kano Ta Arewa A Jam’iyyar APC
Ministan ya ƙara da cewa duk jami’o’in da suka karya wannan doka za su fuskanci hukunci, inda aka umarci shugabannin jami’o’i su daidaita tsarin bayar da digirin. Haka kuma ya ce daga yanzu sai jami’o’i sun nemi amincewar National Universities Commission kafin su bayar da irin wannan digiri.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
