Connect with us

Opinion

“Ba Shekaru A Ofis Ke Nuna Ƙwarewa Ba’ — Muhawara Ta Kunno Kai Kan Waiya Da Garba”

Published

on

IMG 20260622 WA0007

Daga Tijjani Sarki

Kiraye-kirayen da ake yi na a sake bai wa tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Alhaji Muhammad Garba, dama ya koma kan kujerarsa sun janyo muhawara a tsakanin masu ruwa da tsaki a jihar.

Advertisement

Masu goyon bayan Garba na bayyana shi a matsayin gogaggen jami’in gwamnati wanda ya shafe tsawon shekaru takwas yana jagorantar ma’aikatar, tare da ikirarin cewa dawowarsa za ta ƙara wa gwamnati ƙarfi wajen isar da manufofinta ga jama’a.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta musanta zargin yiwa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya

Advertisement

Sai dai wasu na ganin ya dace a yi nazari kan tarihin ayyukan shugabannin biyu maimakon dogaro da suna ko kuma tsawon lokacin da mutum ya yi a kan mukami.

A cewarsu, tambayar da ya kamata a yi ita ce, bayan shekaru takwas da Muhammad Garba ya yi yana jagorantar ma’aikatar, mene ne har yanzu bai kammala ba da ke sa ake neman sake dawo da shi?

Advertisement

Masu wannan ra’ayi sun jaddada cewa ba sa musanta gudunmawar da tsohon kwamishinan ya bayar, amma suna ganin ya kamata a auna shugabanci ne da sakamakon aiki, ba wai da jin daɗin siyasa ko ra’ayoyin magoya baya kawai ba.

Sun kuma ce ƙwarewa ba ta ta’allaka ga tsawon shekarun zama a ofis ba, illa dai tana bayyana ne ta hanyar kirkire-kirkire, cimma manufofi, bunƙasa ma’aikata da cibiyoyi, da kuma iya amsa buƙatun jama’a yadda ya kamata.

Advertisement

Masu sharhin sun ce idan za a yi amfani da ƙwarewa a matsayin ma’aunin tantancewa, to ya zama wajibi a kwatanta abin da kowane bangare ya cimma a lokacin da ya yi a ofis.

Sun yi nuni da cewa yayin da Muhammad Garba ya yi shekaru takwas a matsayin kwamishina, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya bai wuce shekara ɗaya da rabi ba a kan mukamin.

Advertisement

Duk da haka, a cewarsu, an fara ganin sabbin sauye-sauye da ƙarin kuzari a ma’aikatar, musamman a Sashen Harkokin Cikin Gida, wanda suka ce a baya bai samu kulawar da ta dace ba.

Haka kuma, suna ganin ma’aikatar ta ƙara kusanci da jama’a tare da faɗaɗa ayyukanta a fili tun bayan zuwan Waiya.

Advertisement

Ko da yake sun amince cewa ra’ayoyin jama’a kan ayyukan kwamishinan na yanzu na iya bambanta, sun ce ba za a iya musanta cewa ma’aikatar ta samu sabon salo na hulɗa da jama’a da kuma ƙarin bayyana ayyukanta ba.

Saboda haka, masu wannan ra’ayi sun yi kira da a gudanar da muhawara a fili tsakanin shugabannin biyu domin su gabatar da nasarorinsu, ƙalubalen da suka fuskanta da kuma abin da suke da shi na hangen nesa kan makomar ma’aikatar.

Advertisement

Sun bayyana cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na daga cikin muhimman ma’aikatun gwamnati, kasancewar ita ce ke bayyana manufofi da ayyukan gwamnati ga jama’a.

A ƙarshe, sun ce abin da ya kamata ya zama ma’aunin hukunci shi ne tarihin ayyuka da sakamakon da aka samu, tare da barin al’umma su yanke hukunci bisa hujjoji da bayanan da ke gabansu.

Advertisement

 

— Tijjani Sarki ya rubuto daga Kano

Advertisement

responsivecitizensinitiative@gmail.com

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending