Connect with us

News

Ranar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Duniya: Ƙungiyoyi Sun Buƙaci Haɗin Kan Al’umma Don Ceto Matasa a Kano

Published

on

IMG 20260626 120112 044
Advertisements
ads

Ƙungiyoyin farar hula masu yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Jihar Kano sun yi kira ga gwamnati, iyaye, malamai da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai domin daƙile matsalar shaye-shaye, wadda suka bayyana a matsayin babbar barazana ga makomar matasa da ci gaban al’umma.

An bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin gangamin wayar da kai na “My Voice Against Drugs Walk”, da aka shirya domin bikin Ranar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Duniya, ranar da Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta ware a duk shekara domin wayar da kan al’umma kan illolin shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi.

YAƘI DA SHA DA FATAUCIN MIYAGUN ƘWAYOYI A KANO: Gagarumin Aiki Ne Ke Gaban Kwamitin Muhuyi Rimingado

Gangamin ya samu halartar Foundation for a Drug-Free World, Coalition of NGOs Kano, da sauran ƙungiyoyin sa-kai, inda mahalarta suka yi tattaki tare da isar da saƙonnin da ke ƙarfafa matasa su guji shaye-shaye.

Da take jawabi, Maryam Muhammad, daga ƙungiyar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Jihar Kano, ta ce shaye-shaye na ci gaba da lalata rayuwar dubban matasa tare da haddasa matsalolin tsaro, zaman lafiya da tattalin arziki.

Ta ce lokaci ya yi da kowa zai ɗauki nauyin da ya rataya a wuyansa wajen kare matasa daga fadawa cikin shaye-shaye da kuma hana masu safarar miyagun ƙwayoyi samun damar yaudararsu.

Advertisement

“Ba gwamnati kaɗai za ta iya magance wannan matsala ba. Iyaye, malamai, shugabannin addini, ƙungiyoyin al’umma da matasa kansu dole ne su haɗa kai domin kare al’umma daga wannan annoba,” in ji Maryam Muhammad.

A nata jawabin, Ladidi Adamu Abdullahi ta bayyana cewa wayar da kai na daga cikin manyan hanyoyin rage yawaitar shaye-shaye, tana mai kira ga ƙungiyoyi da cibiyoyin ilimi su ci gaba da gudanar da shirye-shiryen ilmantar da matasa kan haɗarin miyagun ƙwayoyi.

Hakazalika, Aisha Haruna Kabuga, daga Ƙungiyar Kare Haƙƙin Yara, ta ce yara da matasa ne suka fi fuskantar haɗarin fadawa cikin tarkon masu safarar miyagun ƙwayoyi, saboda haka ya zama wajibi iyaye su ƙara sa ido kan tarbiyyar ‘ya’yansu.

Ita ma Maryam Hassan ta buƙaci hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki su ƙara tallafa wa shirye-shiryen wayar da kai da kuma samar da cibiyoyin gyaran hali domin taimaka wa waɗanda suka kamu da shaye-shaye su dawo cikin al’umma.

Mahalarta gangamin sun jaddada cewa nasarar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ba za ta samu ba sai an haɗa hannu tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro, ƙungiyoyin farar hula da daukacin al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending