Connect with us

News

Fulani Sun Ƙauracewa Kasuwar Dabbobi Ta Anchau, Inda Suka Koma Falgore Daji

Published

on

1782767907160
Advertisements
ads

Kungiyar ci-gaban garin Falgore daji da ke ƙaramar hukumar Doguwa a Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta farfaɗo da tattalin arzikin yankin ta hanyar ƙarfafa harkokin kasuwanci a Kasuwar Talata ta Falgore, wadda ta shahara wajen cinikin shanu, sauran dabbobi da kuma kayan hatsi.

Shugaban ƙungiyar, Shuaibu Muhammad Akilu, ya bayyana cewa wasu makiyaya Fulani sun yanke shawarar mayar da harkokin cinikinsu zuwa Kasuwar Falgore, bayan sun ƙaurace wa gudanar da kasuwancinsu a Kasuwar Anchau da ke Jihar Kaduna.

Gwamnatin Tarayya Za Ta Sauya Uniform Din Masu Yi Wa Kasa Hidima NYSC

A cewarsa, komawar ‘yan kasuwar za ta taimaka wajen ƙara bunƙasa kasuwar Falgore, da samar da ƙarin damammakin kasuwanci ga mazauna yankin tare da ƙarfafa tattalin arzikin ƙaramar hukumar Doguwa da ma Jihar Kano baki ɗaya.

Ya kuma yi kira ga daukacin Fulani, masu kiwon dabbobi da sauran ‘yan kasuwa daga sassa daban-daban na ƙasar nan da su ci gaba da gudanar da harkokinsu a Kasuwar Falgore, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen dawo da martabar kasuwar a matsayin ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin cinikin dabbobi a yankin Arewa.

Akilu ya jaddada cewa ƙungiyar za ta ci gaba da haɗa kai da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da ci gaban kasuwar da inganta tattalin arzikin al’ummar yankin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending