Connect with us

News

An Kama Wani Mutum Bisa Zargin Fataucin Jaririn Gwaggon biri A Kano ‎

Published

on

WhatsApp Image 2026 07 09 at 18.32.26

‎Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta kama wani mutum da ake zargi da safarar dabbobin daji ba bisa ka’ida ba, tare da ceto wani jaririn Gwaggon biri a wani samame da ta kai a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano.

Hukumar ta bayyana cewa an gudanar da aikin ne a ranar 7 ga watan Yuli bayan shafe makonni ana tattara bayanan sirri da sanya ido kan ayyukan waɗanda ake zargi.

Gwamnatin Tarrayya Ta Sanar Da Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Oyo

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta a ranar Alhamis, hukumar ta ce jami’an Ofishin Musamman na Yaƙi da Fataucin Dabbobin Daji na Sashen Leken Asiri na Kwastam ne suka gudanar da samamen tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Focused Conservation, Rundunar ‘Yan Sandan Kwastam da kuma jami’an Kwastam na Yankin Kano/Jigawa.

Jami’in da ke jagorantar ofishin, Mataimakin Kwanturola na Kwastam, Anuhu Mani, ya ce an garzaya da jaririn gorilar da aka ceto zuwa cibiyar kula da dabbobi, inda ake ba shi kulawar likitoci ta musamman tare da shirin farfaɗo da lafiyarsa.

Ya ce samamen ya kuma yi nasarar daƙile ayyukan wata ƙungiyar da ake zargi da safarar dabbobin daji masu kariya a yankin Kano.

Advertisement

Ya ce bincike kan lamarin na ci gaba da gudana domin gano sauran mutanen da ake zargi da hannu a wannan haramtacciyar harka. Sai dai ya ce hukumar ba za ta bayyana sunan wanda aka kama ko wasu ƙarin bayanai kan samamen ba a yanzu, domin kada hakan ya kawo cikas ga binciken da ake yi.

 

 

PRNIGERIA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending