Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Hallaka ‘Yanta’adda’ Fiye Da 300 A Zamfara

Published

on

1c513a4f 9647 458a b0fa 93a02b95979c 1778948071711

Dakarun sojin Nijeriya sun kashe masu garkuwa da mutane da satar shanu fiye da 300 a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar a wannan makon, kamar yadda wani jami’in jihar ya bayyana ranar Jumma’a.

Dakarun sun kai samame maɓoyar ‘yanbindigar da ke ƙaramar hukumar Gummi a wani aiki na kwanaki biyu lamarin da ya “kai ga kashe ‘yan ta’adda fiye da 300,” kamar yadda kwamishinan watsa labarai na jihar Zamfara Mahmud Muhammad Dantawasa ya bayyana a wata sanarwa.

Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne

Ƙungiyoyin ta’addanci da “ɓarayin daji” da suka ƙware a garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa suna yawan kai hare-hare a arewaci da tsakiyar Nijeriya tare da kisa da kuma ƙaƙaba haraji kan manoma da ke son zuwa gonakinsu.

Abubakar Muhammad, wani mazaunin Gummi, ya ce sojoji da ‘yan sa-kai sun yi arangama da kimanin ɓarayin daji 1,000 da ke ƙauracewa daga sansaninsu tare da ɗaruruwan dabbobi da suka sato da yammacin ranar Laraba zuwa ranar Alhamis.

Dawowar dakaru

Advertisement

“Sojojin da kuma ‘yan sa-kai sun kashe fiye da ɓarayin daji 300 a fafatawar da aka shafe dare zuwa safiya ana yi,” kamar yadda Muhammad ya shaida wa AFP.

Abubakar Kudi-Kasa, wani mazaunin yakin, ya ce samamen ya faru ne da misalin ƙarfe 2130 agogon GMT ranar Laraba, kuma ƙarar harbi da fashewar ababe sun hana garin barci a cikin dare.

“Kawo yanzu sojoji da ‘yan sa-kai sun yi wa ɓarayin daji ƙawanya,” kamar yadda Kudi-Kasa ya shaida wa AFP.

Dakaru sun yi ƙoƙarin mamaye sansanin ɓarayin makonnin biyu da suka wuce, amma dole suka ja da baya domin “tsabar yawan ɓarayi masu makamai da yawa”, in ji Kudi-Kasa.

Wani mazaunin wurin kuma Shehu Dandare ya ba da irin wannan adadin waɗanda suka mutun bayan dakaru sun “daka” ɓarayin.

Muhimmiyar nasara’

Advertisement

A watan Yulin shekarar da ta gabata, sojojin Nijeriya sun kashe aƙalla ɓarayin daji 150 a wani ƙwaton-ɓauna a wani babban ayarin kimanin ɓarayin daji 350 a jihar Kebbi da ke kusa yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Neja mai maƙwabtaka, kamar yadda jami’ai suka bayyana.

Bayan wata ɗaya, rundunar soji ta kashe fiye da ɓarayin daji 100 a ƙaramar hukumar Bukuyum ta jihar Zamfara, inda jiragen yaƙi tare da dakarun ƙasa suka far ma wani taron ɓarayin daji fiye da 400 a wani sansani na daji, in ji wani rahoton tsaron da aka haɗa wa Majalisar Ɗinkin Duniya.

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana samamen wannan makon a matsayin wata “muhimmiyar nasara” a yaƙin da ake yi da laifuka na hare-hare.

Nijeriya, ƙasar da ta fi yawan mutane a Afirka, tana fama da matsaloli na tsaro, ciki har da garkuwa da mutane da ‘yanbindiga ke yi.

Arewa maso gabashin Nijeriya na fama da ta’addanci tun shekarar 2009, daga farko daga hannun Boko Haram, daga baya kuma ƙugiyar Daesh da ta taso daga cikinta.

 

Advertisement

 

 

TRT AFRIKA 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending