News
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane 14 Bisa Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi A Yobe
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Yobe ta kama mutane 14 da ake zargi da safarar da kuma sayar da miyagun ƙwayoyi, bayan wani samame da jami’anta suka kai maboyar masu aikata laifuka a Ƙaramar Hukumar Jakusko.
Mai magana da yawun rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce samamen ya gudana ne a guraren da ake zargin ana harkokin miyagun ƙwayoyi a Kasuwar Buduwa da ke Jakusko.
Dakarun Soji Sun Hallaka ‘Yanta’adda’ Fiye Da 300 A Zamfara
Ya ce an kama waɗanda ake zargin ne yayin da ake zargin suna sayarwa da kuma amfani da miyagun ƙwayoyi. Daga cikin waɗanda aka kama akwai Hamisu Umar (20), Usman Wakili (25), Aliyu Mohammed (20), Hassan Ali (35), Dudduwa Dorsha (27), Adamu Hussaini (27), Sale Adamu (27), Adamu Umaru (25), Babaru Hassan (28), Dangi Maikudi (22), Hassan Audu (29), Abubakar Usman (29), Ahmadu Waziri (23) da Daudu Yusuf (20).
A cewar rundunar, an kuma ƙwace sama da fakiti 300 na miyagun ƙwayoyi iri-iri, ciki har da Tramadol, ƙwayoyin Vega, tabar wiwi da sauran haramtattun ƙwayoyin da doka ta hana.
Sanarwar ta ƙara da cewa bincike kan lamarin na ci gaba, yayin da waɗanda ake zargin ke bai wa jami’an tsaro bayanan da za su taimaka wajen gano tare da cafke sauran waɗanda ake zargi da hannu a wannan haramtacciyar harka. Za a gurfanar da su a gaban kotu bayan an kammala bincike.
-
News1 day ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News5 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
-
News3 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
