News
NELFUND Ya Musanta Zargin Daina Biyan Alawus Ɗin Ƙarshe Wata Ga Ɗalibai
Asusun Bayar da Lamunin Karatu na Ƙasa (NELFUND) ya karyata rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya dakatar da biyan alawus na kula da kai ga ɗaliban da ke cin gajiyar shirin lamunin karatu na Gwamnatin Tarayya.
Hukumar ta bayyana cewa takardar da ake yaɗawa mai ɗauke da kwanan watan 10 ga Yuli, 2026, wadda aka jingina wa Daraktar Sadarwa da Hulɗa da Jama’a, Misis Oseyemi Oluwatuyi, ba ta fito daga NELFUND ba, don haka ta buƙaci jama’a su yi watsi da ita.
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane 14 Bisa Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi A Yobe
A cewar sanarwar, babu wani lokaci da Gwamnatin Tarayya ko NELFUND suka sanar da dakatar da biyan alawus ga ɗaliban da suka cancanci amfana da shirin.
Hukumar ta ce ikirarin da ke cikin takardar cewa ba a saki kuɗaɗen alawus na watannin Mayu, Yuni da sauran watanni ba, ƙarya ce da ba ta da tushe.
Ta ƙara da cewa ana ci gaba da biyan kuɗaɗen makaranta da alawus ga waɗanda suka cika sharuddan shirin kamar yadda doka ta tanada.
-
News1 day ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News5 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
-
News3 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
