Connect with us

News

KANO: Mata Masu Juna Biyu Na Fuskantar Barazana Sakamakon Lalacewar Cibiyar Lafiya A Dambatta

Published

on

6a51f1c132cf3

Mata masu juna biyu a ƙauyen Mai Unguwa da ke ƙaramar hukumar Dambatta a Jihar Kano na fuskantar ƙalubale mai tsanani yayin nakuda, sakamakon lalacewar cibiyar lafiya guda ɗaya da al’ummar ƙauyen ke dogaro da ita, wadda kuma ke rufe aiki da ƙarfe uku na rana saboda ƙarancin ma’aikata da kayan aiki.

Arewa Radio ta ruwaito cewa Lamarin na tilasta wa mata masu juna biyu yin doguwar tafiya zuwa Babban Asibitin Dambatta domin haihuwa, ko kuma su haihu a gida cikin haɗari. Mazauna ƙauyen sun bayyana cewa wannan matsala na ci gaba da jefa rayuwar mata da jarirai cikin barazana, duk da alkawarin gwamnatin jihar na faɗaɗa cibiyoyin lafiya masu aiki na sa’o’i 24.

NELFUND Ya Musanta Zargin Daina Biyan Alawus Ɗin Ƙarshe Wata Ga Ɗalibai

Ɗaya daga cikin waɗanda bala’in ya shafa shi ne marigayiya Nana Asma’u. Mijinta, Iliyasu Isyaku, ya ce matarsa ta fara nakuda bayan ruwa ya fashe da misalin ƙarfe 3:30 na dare, lokacin da cibiyar lafiyar ƙauyen ta riga ta kulle. Ya ce kafin su isa Babban Asibitin Dambatta, ita da jaririn da ke cikinta sun rasu sakamakon wahalar tafiya da jinkirin samun kulawar likita.

Sai dai ba mutuwa kaɗai ce ke damun mazauna ba. Wasu mata sun ce suna tsoron zuwa cibiyar lafiyar saboda mummunan yanayinta. Zainab Jamilu ta ce a wani lokaci yayin da take zaman awo, wani ɓangare na rufin ginin ya fado kusa da inda take zaune, lamarin da ya ƙara razana mata masu neman kulawa.

Jami’in lafiya mai aikin sa kai, Sani Bashiru Mukhtar, ya ce yawan mata masu zuwa awon ciki ya ragu matuƙa saboda rashin amincewa da cibiyar, har wasu magunguna ke ƙarewa ba tare da an yi amfani da su ba. A cewarsa, cibiyar ba ta da isassun kayan aiki kuma tana aiki na sa’o’i biyar kacal a rana.

Advertisement

Shugaban Ƙungiyar Cigaban Ƙauyen Mai Unguwa, Atiku Sulaiman, ya bayyana cewa al’umma sun sayi katinan asibiti 1,000 domin ƙarfafa wa jama’a gwiwar neman kulawar lafiya. Sai dai ya ce duk da koke-koken da suka sha kai wa hukumomi, har yanzu ba a samu gagarumin sauyi ba.

Rahotanni sun nuna cewa an gina cibiyar lafiyar fiye da shekara 20 da suka gabata, amma yanzu tana cikin mummunan hali. Bangon ginin ya tsage, yayin da kadangaru da sauran dabbobi ke shiga ciki, sannan kashin jemagu ya mamaye wasu sassan ginin.

Wata mazauniyar ƙauyen, Rabi Nura, ta ce ta yanke shawarar zuwa Asibitin Kwararru na Dambatta idan nakuda ta same ta, domin cibiyar lafiyar ƙauyen ba ta da damar karɓar haihuwa.

Bisa alkaluman Hukumar Kula da Lafiya ta Matakin Farko ta Ƙasa, a shekarar 2024 Najeriya na rasa kusan yara 2,300 masu ƙasa da shekara biyar da kuma mata 145 masu shekarun haihuwa a kowace rana.

A martaninta, Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana ci gaba da inganta harkokin lafiya a faɗin jihar. Kwamishinan Lafiya, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce gwamnati ta riga ta gyara cibiyoyin lafiya 320, tare da shirin faɗaɗa aikin zuwa cibiyoyi 484 domin su rika aiki sa’o’i 24 a kowace rana.

Sai dai ga mazauna ƙauyen Mai Unguwa, suna ganin mafita ita ce a gaggauta gyara cibiyar lafiyarsu tare da samar da isassun ma’aikata da kayan aiki, domin tabbatar da cewa duk mace mai nakuda ta samu kulawar gaggawa ba tare da fuskantar barazanar rasa ranta ko na jaririnta ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending