News
INEC Ta Tsawaita Wa’adin Gabatar da Sunayen ‘Yan Takara Zuwa 14 Ga Yuli
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da tsawaita wa’adin da ta bai wa jam’iyyun siyasa na gabatar da sunayen ‘yan takararsu domin zaɓukan shekarar 2027 da ƙarin kwanaki uku.
A cewar hukumar, wa’adin da tun farko zai ƙare a ranar Asabar, 11 ga Yulin 2026, yanzu an tsawaita shi zuwa tsakar daren ranar Talata, 14 ga Yulin 2026.
Rashin Halartar Kwamishinan Yaɗa Labarai Ya Jawo Ce-ce-ku-ce A Taron Arewa Media Summit
INEC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, wadda Kwamishinan Hukumar kuma Shugaban Kwamitin Wayar da Kan Masu Kaɗa Ƙuri’a da Ilimantar da Su, Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne bayan ƙorafin da Majalisar Ba da Shawarwari Tsakanin Jam’iyyun Siyasa (IPAC) ta gabatar a madadin wasu jam’iyyun siyasa da suka ce ba su samu damar kammala loda sunayen ‘yan takararsu da sauran bayanan da ake buƙata cikin wa’adin da aka tanada ba.
“Hukumar ta amince da tsawaita wa’adin ne domin bai wa waɗannan jam’iyyu damar kammala gabatar da bayanan ‘yan takararsu kafin cikar sabon wa’adin,” in ji sanarwar.
INEC ta jaddada cewa matakin ya yi daidai da ƙudirinta na tabbatar da dukkan jam’iyyun siyasa sun samu damar shiga tsarin zaɓe cikin adalci, tare da kiyaye tanade-tanaden dokokin zaɓe.
Har ila yau, hukumar ta yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da su yi amfani da ƙarin kwanakin da aka ba su wajen kammala loda sunayen ‘yan takara da sauran bayanan da ake buƙata kafin tsakar daren ranar 14 ga Yulin 2026, domin kauce wa rasa wa’adin da aka sake tsarawa.
-
News4 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
-
News2 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News2 days ago
Gwamnatin Kano Ta Ayyana 1 Ga Satumba A Matsayin Ranar Hutun Bikin Takutaha
