Connect with us

News

SERAP Ta Kai INEC Kotu Kan Zargin Karkatar da Naira Biliyan 800 Domin Harkokin Siyasa

Published

on

Kungiyar kare hakkin tattalin arziki da tabbatar da gaskiya da rikon amana (SERAP) ta shigar da kara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), tana neman a tilasta wa hukumar binciken wasu zarge-zarge da ake yi kan wasu gwamnonin jam’iyyar APC.

SERAP ta ce ana zargin gwamnonin sun karkatar da kimanin naira biliyan 800 daga kudaden rabon Asusun Tarayya (FAAC) domin gudanar da harkokin siyasa da kuma shirye-shiryen yakin neman zabe.

Rashin Halartar Kwamishinan Yaɗa Labarai Ya Jawo Ce-ce-ku-ce A Taron Arewa Media Summit

A wata sanarwa da Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya fitar a ranar Lahadi, kungiyar ta bayyana cewa an shigar da karar ne a makon da ya gabata domin neman kotu ta umurci INEC ta gudanar da bincike kan lamarin.

Kungiyar ta ce rahotannin da suka bayyana a kafafen yada labarai sun yi zargin cewa wasu gwamnonin APC na ware wani bangare na kudaden da jihohinsu ke karba daga Asusun Tarayya (FAAC), suna tura su zuwa wani asusun yakin neman zabe da ake zargin za a yi amfani da shi wajen tallafa wa yakin neman sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.

A cikin karar, SERAP ta bukaci kotu ta umurci INEC ta binciki zarge-zargen, tare da tilasta wa jam’iyyar APC da gwamnoninta bayyana cikakken bayani kan kudaden da aka bayar, wadanda suka bayar da gudunmawar da kuma asalin kudaden.

Advertisement

Har ila yau, kungiyar ta nemi a tantance ko an bi tanadin Sashe na 91 na Dokar Zabe, wanda ya shafi tara da amfani da kudaden yakin neman zabe.

SERAP ta ce binciken irin wadannan zarge-zarge yana da muhimmanci domin tabbatar da gaskiya, adalci da rikon amana a tsarin zaben kasar nan, tare da kare martabar dimokuradiyya.

Zuwa lokacin kammala wannan rahoto, INEC da jam’iyyar APC ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da karar da SERAP ta shigar ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending