News
Wasu Ɓata Gari Sun Hallaka Mai Sayar Da Shayi A Kano
Wani magidanci mai sana’ar sayar da shayi, Mallam Yahaya, ya mutu bayan da wasu da ake zargin ‘yan fashi ne suka caka masa wuka tare da kwace babur ɗinsa a unguwar Ƙofar Nasarawa da ke Jihar Kano.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a daren Litinin, 13 ga Yuli, 2026, lokacin da ake ruwan sama. An ce maharan sun bi marigayin tun daga yankin Ƙofar Nasarawa, kafin su tare shi a kusa da gidan Zoo, inda suka caka masa wuka, abin da ya yi sanadin rasuwarsa.
Gwamnatin Kano Ta Musanta Rahoton Alƙaluma Kan Yawan Jama’a, Masana’antu da Masallatai
Majiyoyi sun bayyana cewa bayan sun aikata harin, maharan sun tsere da babur mai ƙafa biyu na marigayin.
Lamarin ya tayar da hankalin mazauna yankin, inda suka yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara tsaurara sintiri, musamman daga ƙarfe tara na dare zuwa wayewar gari.
Sun ce a baya-bayan nan wasu ɓata gari na amfani da dare wajen tare matafiya da kwace musu babura da sauran kayayyaki masu daraja, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
-
News4 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
-
News2 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News3 days ago
Gwamnatin Kano Ta Ayyana 1 Ga Satumba A Matsayin Ranar Hutun Bikin Takutaha
