Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Tilastawa Mazauna Ƙauyukan Tserewa Daga Gidajensu A Benue

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Ankpechi da ke karamar hukumar Ohimini a Jihar Benue, inda suka tilasta wa mazauna yankin tserewa zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu.

Rahotanni sun ce harin ya faru ne da safiyar Alhamis tsakanin karfe 8:00 zuwa 9:00 a yankin Ankpechi da ke gundumar Oglewu, kan hanyar Otukpo zuwa Ogobia.

Kotu Ta Ɗaure Matashi Shekara 7 Kan Tallata Wiwi A Soshiyal Midiya A Kano

A yayin harin, maharan sun rika bude wuta ba kakkautawa, lamarin da ya yi sanadin jikkatar mutum guda, wanda ke samun kulawar likitoci a asibiti.

Shugaban karamar hukumar Ohimini, Gabriel Adole, ya bayyana cewa binciken farko ya nuna maharan sun kai harin ne domin sace kayan abinci, inda suka fasa shaguna tare da kwashe kayayyaki.

Wannan hari ya biyo bayan wani mummunan farmaki da aka kai a makwabciyar karamar hukumar Otukpo kwanaki biyu da suka gabata, inda aka kashe tsakanin mutane 16 zuwa 18.

Advertisement

Lamarin ya haddasa zanga-zangar matasa, yayin da wani basarake a yankin ya ba da umarnin korar makiyaya daga wasu sassan yankin.

Haka kuma, a ranar Talata maharan sun sake kai hari kauyen Ondo da ke yankin Ugboju, abin da ya tilasta wa iyalai da dama barin gidajensu saboda fargabar hare-hare.

A halin yanzu, jami’an tsaro na hadin gwiwa sun bazama cikin dazukan da ke kewaye da yankin domin farautar maharan da kuma dawo da zaman lafiya.

 

 

RFI HAUSA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending