News
YOBE: Ruwa Da Iska Mai Ƙarfi Sun Hallaka Mutum Uku Tare Da Lalata Gidaje Da Dukiyoyi A Nguru
Aƙalla mutum uku sun rasa rayukansu bayan ruwan sama mai ƙarfi haɗe da guguwar iska sun yi mummunar barna a wasu unguwanni da ke Ƙaramar Hukumar Nguru a Jihar Yobe.
Bala’in ya faru ne cikin dare, inda ya lalata gidaje da dama tare da jikkata wasu mutane, sannan ya tilasta wa ɗaruruwan mazauna yankin barin gidajensu.
‘Kano Na Buƙatar Sabbin Ayyuka, Ba Sake Tallata Tsofaffi Ba’ — Tijjani Sarki
Rahotanni sun ce unguwannin Tsohon Nguru da Filing Idi na daga cikin wuraren da guguwar ta fi yin barna.
Wani mazaunin yankin, Bukar Adamu, ya shaida wa Daily Trust cewa gidaje, katanga da sauran dukiyoyi sun lalace sakamakon ƙarfin iska da ruwan saman.
Ya ce iyalai da dama sun koma gidajen ‘yan uwansu, yayin da wasu kuma suka samu mafaka a wasu gine-ginen gwamnati.
Bukar ya yi kira ga gwamnatin jihar da masu hannu da shuni da su gaggauta kai wa waɗanda abin ya shafa agajin gaggawa.
Shi ma wani mazaunin yankin, Mustapha Modu, ya ce guguwar ta lalata gidaje, shaguna da rumfunan kasuwa, tare da haddasa asarar dukiyoyi masu yawa.
Ya bayyana cewa wani yaro mai suna Ilya Alhassan daga unguwar Filing Idi ya rasu bayan wani ɗaki ya rufta masa a lokacin da guguwar ke tafiya.
A halin yanzu, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (YOSEMA) ta fara tantance irin barnar da aka yi da kuma adadin mutanen da bala’in ya shafa.
Wani jami’in hukumar ya ce ana tattara bayanan gidaje da dukiyoyin da suka lalace domin gwamnati ta tsara yadda za a kai agaji ga waɗanda abin ya shafa.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
