Connect with us

News

An Gano Gawa Ɗaya Bayan Kwale-Kwale Ya Kife Da Mutane 40 A Jigawa

Published

on

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Ringim da ke Jihar Jigawa sun bayyana cewa an gano gawar mutum ɗaya daga cikin mutane kusan 40 da wani kwale-kwale ya kife da su a yankin Malamawa.

Lamarin, wanda ya faru a ranar Lahadi, ya rutsa da mata da yara da dama, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin ceto domin gano sauran fasinjojin da har yanzu ba a san inda suke ba.

Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Mutunta Bukatar Iyalan Mary Habila Na Binne Ta Cikin Sirri

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa, SP Shi’isu Lawan Adam, ya tabbatar da aukuwar hatsarin. Ya ce an gano gawa ɗaya zuwa yanzu, yayin da jami’an tsaro tare da masu aikin ceto ke ci gaba da bincike da neman sauran mutanen da hatsarin ya shafa.

Haka kuma, Masarautar Ringim ta tabbatar da faruwar hatsarin, inda ta bayyana cewa lamarin ya yi sanadin asarar rayuka, sai dai ba ta bayyana adadin waɗanda suka rasu ba.

Majiyoyi daga yankin sun ce matasa da mazauna ƙauyukan da ke kusa sun haɗa kai da jami’an tsaro wajen gudanar da aikin ceto da kuma neman waɗanda har yanzu ba a gano ba.

Advertisement

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomi ba su fitar da cikakken adadin waɗanda suka tsira ko waɗanda suka rasa rayukansu ba. Sai dai sun sake yin kira ga masu amfani da hanyoyin sufurin ruwa da su bi ƙa’idojin tsaro.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending