News
Shugaba Tinubu Ya Amince Da Faɗaɗa Rundunar Sojin Ƙasa zuwa Divisions 12, Za A Ɗauki Sabbin Sojoji 28,000
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da faɗaɗa tsarin Rundunar Sojin Ƙasan Najeriya (Nigerian Army) daga Divisions takwas zuwa goma sha biyu, a wani mataki da gwamnati ta ce zai ƙara ƙarfafa tsaron ƙasa da inganta yadda rundunar ke gudanar da ayyukanta.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis.
Jihar Kano Ta Shirya Tsaf Domin Kafa ’Yansandan Jiha — Gwamna Abba Kabir Yusuf
A cewar sanarwar, wannan mataki na nuna ƙudirin gwamnatin Tinubu na ci gaba da ƙarfafa rundunonin tsaro domin fuskantar ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fama da su.
Baya ga faɗaɗa tsarin rundunar, Shugaban Ƙasar ya kuma amince da ɗaukar sabbin sojoji 28,000, tare da sayen sabbin kayan aikin soja, inganta walwalar jami’ai da sojoji, da kuma ci gaba da zamanantar da rundunar.
Sabon tsarin zai sa rundunar ta kasance da Divisions 12 da za su rika kula da jihohi daban-daban na ƙasar. Sabbin hedikwatocin da za a kafa sun haɗa da Makurdi (Division ta 5), Ilorin (Division ta 9), Jalingo (Division ta 10), da Benin City (Division ta 83).
Gwamnatin ta bayyana cewa kafa waɗannan sabbin divisions zai taimaka wajen kusantar da shugabancin ayyukan soja zuwa yankuna, saurin yanke hukunci, ƙarfafa tsaron kan iyakoki, kare muhimman kadarorin gwamnati, da kuma inganta yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro.
Za a aiwatar da wannan sabon tsari ne a matakai biyu. Mataki na farko, wanda ya haɗa da kafa Divisions na 5, 9 da 10 tare da sake fasalin wasu rundunoni, ana sa ran kammala shi kafin watan Satumban 2026.
Mataki na biyu kuwa, wanda ya haɗa da kafa Division ta 83 da sauran gyare-gyare, ana sa ran kammala shi kafin ƙarshen watan Disamban 2026.
Shugaba Tinubu ya yabawa Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Ibrahim Shuaibu, da dakarun rundunar saboda jajircewarsu wajen kare haɗin kan ƙasa da martabar Najeriya.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a rundunonin tsaro domin tabbatar da suna da ingantattun kayan aiki, kwarin gwiwa, da cikakken ƙarfi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Najeriya.
-
Opinion4 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion4 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News2 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
