Connect with us

News

KACCIMA Za Ta Karɓi Bakuncin Gasar Masu Ƙananan Sana’o’i  Da Matashiya TV Ta Shirya A Kano 

Published

on

IMG 20260804 WA0020

Matashiya TV za ta yi haɗin gwiwa da cibiyar kasuwanci, masa’antu, ,a’adanai da aikin gona ta Kano don shirya gasar sana’o’i ta matasa a watan Agustan 2026.

Shugaban majalisar ƴan kasuwa da masu sana’o’i ta jihar Kano Alhaji Hassan Yaro ne ya bayyana haka a wata tattaunawa ta musamman tare da tsara yadda shirin zai kasance yau Talata.

Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ƙarin Albashin Kashi 80 Ga Dakarun Soji 

Ya ce za a bijiro da tsare-tsare da za su taimakawa ƙananan ƴan kasuwa da masu sana’o’i don a ƙarfafa musu gwiwa ta yadda za su ci gaba da dogaro da kansu.

Sannan waɗanda su ka shiga gasar na iya samun tagomashi don a yi musu rijista kyauta a gwamnatin tarayya a hukumance don ƙara zamanantar da sana’o’insu.

Shirin gasar wanda Matashiya ta shirya a wani bangare na bikin cika shekara goma bayan kammala bayar da horo da Matashiya TV ta yi wa matasa da mata a ɓangare daban-daban don su dogara da kansu.

Advertisement

Idan za ku iya tunawa shugaban rukunin kamfanonin Ammasco Alhaji Mustapha Ado Muhammad ma ya sha alwashin bayar da gagarumar gudunmawa a cikin shirin.

Dgaa ciki akwai mota da za ta haska yadda gasar za ta kasance kai tsaye.

Har yanzu matasa na da damar shiga gasar kamar yadda a ka tsara, kuma za a rufe shiga a ranar Juma’a 7/8/2026 daga bisani kuma a sanar da rana da lokacin yin gasar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending