News
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
Rundunar ’Yansandan Najeriya ta tura kwamishinonin ’yansanda 30 da sama da jami’ai 15,000 domin tabbatar da tsaro yayin zaɓen gwamnan Jihar Osun da za a gudanar ranar Asabar.
Rundunar ta kuma bayyana cewa Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda (DIG) zai jagoranci ayyukan tsaro na zaɓen, yayin da za a yi amfani da jiragen sama masu saukar ungulu da jirage marasa matuƙa (drones) wajen sa ido a faɗin jihar.
Yara 875,593 Ne Ba Sa Zuwa Makaranta A Kano — Gwamnati
Kakakin rundunar, CSP Anietie Iniedu, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a Osogbo, babban birnin Jihar Osun, kan shirye-shiryen tsaron zaɓen.
Ya ce an fara tura jami’ai da kayan aikin tsaro zuwa jihar makonni uku kafin zaɓen, domin samar da isasshen tsaro a ƙananan hukumomi 30 na jihar.
A cewarsa, kowace ƙaramar hukuma za ta samu kwamishinan ’yan sanda, mataimakin kwamishinan ’yan sanda, kwamandan Mobile Police da kuma kwamandan Police Mobile Force (PMF).
“Mun tura ’yan sandan Mobile Force masu ɗauke da makamai zuwa kowace ƙaramar hukuma. Muna da rundunoni 30 a ƙananan hukumomi 30, kuma kowace runduna tana da kusan jami’ai 60,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa an tura rundunonin PMF guda biyu, kowannensu na ɗauke da sama da jami’ai 60, zuwa hedikwatar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ke Osogbo.
Iniedu ya ce jirgin sama mai saukar ungulu da rundunar drones sun isa Osogbo, inda za su gudanar da sa ido kafin zaɓe, yayin zaɓe da kuma bayan kammala zaɓen.
Haka kuma, ya bayyana cewa Sojoji za su rufe hanyoyin da ke shiga jihar daga tsakar daren ranar Asabar, domin takaita zirga-zirgar ababen hawa a lokacin zaɓen.
Ya ce za a bar zirga-zirga ne kawai ga masu gudanar da ayyukan gaggawa, jami’an tsaro da masu zuwa kada kuri’a.
A cewarsa, zuwa yanzu rundunar ta kwato bindigogi haramtattu kusan 34 a Jihar Osun, yayin da bincike kan makaman ke ci gaba.
Gwamna Ademola Adeleke na Accord, Bola Oyebamiji na APC da Najeem Salaam na ADC na daga cikin manyan ‘yan takarar da ke fafutukar neman kujerar gwamnan jihar.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
