News
ICPC Ta Gano Wani Jami’in Da Ya Sanya Matarsa, ’Ya’yansa Da ’Yan Uwansa 14 Cikin Masu Karɓar Albashin Gwamnati
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifukan da Suka Shafi Hakan (ICPC) ta ce ta gano wani jami’in gwamnati da ya sanya sunayen ’yan uwansa 14 cikin jerin masu karɓar albashin gwamnati.
Shugaban hukumar, Musa Aliyu, ya bayyana hakan ne a wajen taron Economic Confidential Lecture and National Spokespersons Award 2026, wanda aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
Aliyu ya ce binciken da hukumar ta gudanar ya gano yadda wasu jami’an gwamnati ke amfani da guraben da ke cikin tsarin biyan albashi wajen shigar da sunayen ƙagaggun ma’aikata domin karɓar albashin da bai dace da su ba.
Ya ce a wani lamari da hukumar ta gano, mutum guda ya sanya sunayen mutane 14 daga cikin iyalinsa cikin jerin masu karɓar albashin gwamnati.
“Mun gano wani mutum da ya sanya mutane 14 daga cikin iyalinsa. Yana zaune a wani otel, yana karɓar albashi,” in ji shugaban ICPC.
Ya kuma bayyana cewa an gano wani mutum da ya sanya matarsa, ’yarsa, ɗansa da wasu ’yan uwansa cikin tsarin albashin gwamnati, inda shi kaɗai ke karɓar albashin mutane 13 a kowane wata.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
