News
Mutane 30 sun mutu A Bayan Zaftarewar Ƙasa A Wurin Zubar Da Shara
Akalla mutane 30 ne suka mutu, yayin da wasu 22 suka jikkata sakamakon zaftarewar ƙasa a wani wurin zubar da shara a babban birnin Guinea, Conakry.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na safiyar Lahadi a yankin Dar es Salam da ke Gbessia, bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka shafe dare ana yi.
Gwamnatin Guinea ta ce zaftarewar ƙasar ta haddasa rugujewar gidaje da dama, tare da binne wasu mutane a ƙarƙashin tarkace.
Hukumomin tsaro sun ce daga cikin mutum 22 da suka jikkata, shida sun samu munanan raunuka, yayin da 16 suka samu ƙananan raunuka.
Gwamnati ta tura kayan aikin ceto zuwa wurin domin ci gaba da aikin neman mutanen da ake zargin suna ƙarƙashin tarkacen ƙasa, tare da ceto waɗanda suka tsira.
Firaministan Guinea, Amadou Oury Bah, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda ya tabbatar da cewa gwamnati na ɗaukar matakan gaggawa domin kula da waɗanda suka jikkata da kuma tallafa wa waɗanda bala’in ya shafa.
Tsohon Firaministan ƙasar kuma jagoran ‘yan adawa, Cellou Dalein Diallo, ya bayyana lamarin a matsayin babban bala’i da ya jefa al’umma cikin jimami.
Diallo ya ce lamarin ya fi tayar da hankali saboda an shirya rufe wurin zubar da sharar a ranar Lahadi, 23 ga Agusta.
Ya bukaci hukumomi su gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin bala’in da kuma tabbatar da lafiyar mazauna yankin.
A ‘yan kwanakin baya ne gwamnatin Guinea ta sanar da matakan kwashe jama’a daga wasu yankunan da ke kusa da wurin zubar da shara saboda barazanar zaftarewar ƙasa.
Janar Mamadi Doumbouya ne ke jagorantar Guinea, bayan ya karɓi mulki ta hanyar juyin mulki a shekarar 2021.
