Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Sabon Tsarin Samar Da Tsaro, Za Ta Ƙara Tura Makamai Da Motoci Kano

Published

on

1788303919144

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin ƙara tura makamai, motocin yaƙi da sauran kayan aikin tsaro zuwa Jihar Kano, domin ƙarfafa yaƙi da ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro.

Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin lokacin da ya kai ziyarar jaje da duba halin tsaro ga Gwamnatin Jihar Kano, bayan harin da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Chiroma da ke Ƙaramar Hukumar Garun Mallam a ranar 29 ga Agusta, 2026.

KANO : ’Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam’iyyar APC Na Rogo

Matawalle ya ce Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa wani kwamiti domin tsara Shirin Tsaro da Kare Ƙasa na Shekaru Biyar, wanda zai samar da tsarin dogon lokaci na tunkarar barazanar tsaro da ke fuskantar ƙasar.

Ya ce gwamnatin tarayya za ta kuma ƙara haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi, tare da ƙarfafa musayar bayanan sirri tsakanin jami’an tsaro da al’umma.

“Shugaban Ƙasa ya kafa kwamiti domin samar da Shirin Tsaro da Kare Ƙasa na Shekaru Biyar. Wannan shiri zai jagoranci yadda za mu tunkari barazanar tsaro a faɗin ƙasar nan na dogon lokaci,” in ji Matawalle.

Advertisement

Ministan ya kuma tabbatar wa gwamnatin Kano cewa za a samar da ƙarin motocin yaƙi, makamai da sauran kayan aikin da ake buƙata domin ƙarfafa ayyukan jami’an tsaro a jihar.

Ya bayyana cewa bayan harin Garun Mallam, Kwamandan Brigade na 3 da ke Kano, Birgediya Janar Jimoh, ya jagoranci wani samamen ceto tare da jami’an Rundunar Haɗin Gwiwa (JTF) daga sansanonin Hawan-Kwano da Kwanar Dangora.

A cewarsa, aikin ya kai ga ceto wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a yankunan gadar Yan-Kifi da Marabar Kwari da ke Garun Mallam.

Matawalle ya yaba wa jami’an tsaron bisa gaggawar da suka mayar da martani ga harin, yana mai cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ƙarfafa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro da kayan aiki domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma jaddada cewa nasarar yaƙi da rashin tsaro na buƙatar haɗin gwiwar gwamnatin tarayya, jihohi, ƙananan hukumomi da kuma al’umma, musamman wajen samar da sahihan bayanan sirri ga jami’an tsaro.

A nasa ɓangaren, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gode wa ministan bisa ziyarar, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da haɗa hannu da gwamnatin tarayya domin ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano.

Advertisement

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending