News
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
An bayyana Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, a matsayin ɗan siyasa mai haƙuri da biyayya, wanda haɗin gwiwarsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taimaka wajen ciyar da manufofin gwamnatin tarayya gaba.
Babban Daraktan Kudi na Hukumar Raya Kogin Hadejia-Jama’are (HJRBDA), Alhaji Musa Illiyasu Kwankwaso, ne ya bayyana hakan a cikin saƙon taya murnar cikar Mataimakin Shugaban Ƙasar shekaru 60 da haihuwa.
FBI Ta Tabbatar An Taba Tuhumar Tinubu Kan Safarar Hodar Ibilis Da Halasta Kudaden Haramun
Kwankwaso ya ce haɗin gwiwar da ke tsakanin Shettima da Shugaba Tinubu ya taimaka wajen ƙarfafa haɗin kan ’yan Najeriya, musamman tsakanin al’ummomi da ƙabilu daban-daban.
Ya ce irin wannan haɗin kai ya kuma taimaka wajen wargaza wasu ra’ayoyi da ake da su na cewa akwai rashin jituwa tsakanin Shugaban Ƙasa da Mataimakinsa.
“Haɗin gwiwarka da Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya kasance muhimmi wajen ciyar da ajandar Renewed Hope gaba da kuma aiwatar da sauye-sauyen da gwamnatin ke yi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ƙwarewar Shettima a harkokin siyasa, gogewarsa da kuma iya samar da fahimtar juna sun taimaka wajen ƙarfafa ƙoƙarin gwamnatin tarayya na samun ci gaba mai ɗorewa.
Kwankwaso ya ce cikar Shettima shekaru 60 wata dama ce ta yaba da irin gudunmawar da ya bayar wajen hidimtawa ƙasa, yana mai bayyana shi a matsayin ɗan ƙasa mai kishin Najeriya.
Ya ce rayuwar Shettima a hidimar jama’a ta nuna jajircewa, tawali’u da zurfin tunani, tare da ƙudurin ganin Najeriya ta samu ci gaba.
Haka kuma, ya yaba da gudunmawar Mataimakin Shugaban Ƙasar wajen ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiyar jam’iyyar APC, yana mai cewa hakan na taimakawa wajen ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar.
“Za mu ci gaba da ba ka goyon baya, tare da tallafa wa gwamnati wajen ƙarfafa zaman lafiya, wadata da ci gaban ƙasa,” in ji Kwankwaso.
Ya kuma yi wa Mataimakin Shugaban Ƙasar fatan alheri da samun ƙarin nasara, tare da addu’ar Allah Ya ba shi lafiya da hikimar ci gaba da gudanar da ayyukansa na hidimar ƙasa.
Kwankwaso ya ce shi da sauran masu kishin ƙasa za su ci gaba da yin koyi da kyawawan halayen Shettima tare da yi masa addu’ar samun nasara, da kuma fatan gwamnatin Shugaba Tinubu ta cimma manufofinta na inganta rayuwar ’yan Najeriya.
