News
INEC Ta Sanya Ranar Zaɓen Cike Gurbi A Jihohin Kano, Gombe, Bauchi Da Delta
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026, domin gudanar da zaɓen cike gurbi a jihohin Kano, Gombe, Bauchi da Delta.
Sakataren Yaɗa Labaran Hukumar, Tunde Oketola, ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ranar Talata a Abuja.
Jami’an Ƴansanda Sun Ceto Yara 17 Da Aka Sace A Oyo
A Jihar Kano, za a gudanar da zaɓen cike gurbin kujerar Majalisar Dokokin Jihar da ke wakiltar Dawakin Kudu.
A Gombe kuwa, za a gudanar da zaɓen cike gurbin kujerar Majalisar Wakilai ta tarayya mai wakiltar Gombe/Kwami/Funakaye.
Hukumar ta ce zaɓen zai kuma gudana a wasu kujeru da suka zama babu kowa a jihohin Bauchi da Delta.
INEC ta bayyana cewa shirya zaɓen na daga cikin matakan da take ɗauka domin cike guraben kujerun siyasa da suka zama babu kowa kafin babban zaɓen 2027.
Hukumar ta ƙara da cewa za ta sanar da ƙarin bayanai kan tsarin gudanar da zaɓen da sauran shirye-shiryen da suka shafi zaɓen a lokacin da ya dace.
