News
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wani Mutum Ya Na Kokarin Sayar Da ‘Yarsa Yar Watanni 16
Rundunar ’yansandan Jihar Abia ta ce ta kama wani mutum tare da wasu mutum uku bisa zargin ƙoƙarin sayar da ’yarsa ta cikinsa mai watanni 16 domin samun kuɗi.
An kama mutanen huɗun ne a wani otal da ke Obi, ƙaramar hukumar Obingwa, ranar 7 ga Satumba, 2026, yayin da jami’an Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) na rundunar ke gudanar da aiki.
An Hallaka Matashin Da Ya Kai Wa Sheikh Musa Lukuwa Hari A Sakkwato
Kwamishinan ’yansandan jihar, Wilfred Afolabi, ya ce binciken farko ya tabbatar da cewa yarinyar ’yar wanda ake zargin ce, yayin da aka gano cewa manufar safarar ta ita ce samun kuɗi.
An ceto yarinyar kuma an miƙa ta hannun Ma’aikatar Harkokin Mata ta jihar, yayin da ake tsare da waɗanda ake zargin domin ci gaba da bincike.
Kwamishinan ya kuma ce tun bayan hawansa ofis a ranar 10 ga Agusta, rundunar ta samu rahotannin laifuka sama da 152 tare da kama mutane sama da 220, inda aka ceto mutane tara da aka sace tare da kwato harsasai 101 da motoci shida da aka sace.
