Connect with us

News

Wani Ƙani Ya Yi Wa Yayansa Yankan Rago Saboda Rigar Singileti A Zariya

Published

on

Wani matashi mai suna Aliyu Abubakar, mai shekaru 23, ana zarginsa da kashe yayansa, Hafis Abubakar, mai shekaru 25, sakamakon wata takaddama da ta shafi rigar singileti a Unguwar Kwangila, Ƙaramar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a Layin Wakili da ke yankin Kwangila Ƙasan Gada, inda ake zargin Aliyu ya yi amfani da wuƙa wajen ji wa yayansa rauni a maƙogwaro, wanda daga bisani ya yi sanadin mutuwarsa.

An Kama Likita Da Mahaifiya Kan Zargin Sayar Da Jaririya

Da yake magana kan lamarin, Dakacin Kwangila, Alhaji Ya’u Shehu, ya bayyana cewa ’yan uwan suna da uba ɗaya, wanda ya rasu.

Ya ce bayan samun labarin abin da ya faru, sun garzaya gidan, inda suka tarar da Hafis kwance cikin jini.

A cewarsa, sun yi ƙoƙarin kai shi asibiti domin samun kulawar likitoci, amma daga bisani ya rasu.

Advertisement

Dakacin ya ƙara da cewa ba su tarar da wanda ake zargi da aikata laifin a gidan ba, yayin da mahaifiyarsu ma ta bar wurin.

Wata kishiyar mahaifiyarsu, wadda ta shaida abin da ya faru, ta bayyana cewa rigimar ta samo asali ne daga takaddamar rigar singileti, inda ta ce ’yan uwan sun daɗe suna samun saɓani a tsakaninsu.

Ta ce a kwanakin baya rikicin ya ƙara tsananta, inda ake yawan samun saɓani tsakaninsu, har ma da zargin cin zarafin mahaifiyarsu.

A cewarta, ranar da lamarin ya faru, Aliyu ya fara zagin mahaifiyarsu, lamarin da ya sa Hafis ɗaukar wani abu da ake kira gariyo domin hana shi ci gaba da zaginta da kuma barazanar da ake zargin ya yi mata.

Ta ce a lokacin da Hafis ya tunkari ƙaninsa, Aliyu ya yi amfani da wuƙar da ke hannunsa ya ji masa rauni a maƙogwaro.

Ta ƙara da cewa sun yi ihu domin neman agaji, amma kafin mutane su iso, Aliyu da mahaifiyarsu, A’isha Abubakar, sun bar gidan.

Advertisement

Wasu maƙwabta sun shaida wa Aminiya cewa ’yan uwan sun daɗe suna samun saɓani, inda suka yi zargin cewa ana yawan samun su cikin halin da suka danganta da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi. Sai dai ba a samu tabbaci daga hukumomi kan wannan zargi ba.

Wani maƙwabci ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga zargin da Aliyu ya yi cewa yayansa yana ɗaukar masa kayansa, ciki har da rigar singileti, duk lokacin da ya ajiye su.

Ya ce rikicin ya ƙara kamari ne bayan Aliyu ya fara zagin mahaifiyarsu, lamarin da ya kai ga fafatawar da ta ƙare da mutuwar Hafis.

A nasa ɓangaren, babban jami’in ’yan sanda na shiyyar Sabon Gari ya tabbatar da kama mahaifiyar ’yan uwan, A’isha Abubakar, yayin da wanda ake zargi da aikata kisan ya tsere.

Ya ce rundunar tana ci gaba da ƙoƙarin cafke wanda ake zargin, tare da faɗaɗa bincike kan lamarin.

Haka kuma, ya bayyana cewa an aika da bayanan lamarin zuwa babban ofishin rundunar da ke Kaduna domin ɗaukar matakan da suka dace.

Advertisement

Ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mansur Hassan, bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran waya ba, kuma ba a samu martaninsa kan saƙon da aka aika masa ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending