News
Al’umma Ne Ke Da Ikon Zaɓen Shugabanni, Ba Jam’iyyun Siyasa Ba – Farfesa Fagge

Wani masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce al’umma ne ke da ikon zaɓen shugabannin da za su jagorance su, ba jam’iyyun siyasa ba.
Farfesa Fagge ya bayyana cewa jam’iyyun siyasa ba su ne ke da ikon yanke wa al’umma wanda zai zama shugabansu ba, illa al’umma ce ke da hurumin zaɓar wanda suke ganin ya dace da shugabancinsu ta hanyar ƙuri’unsu.
’Yan Sanda Sun Gargaɗi ’Yan Siyasa Kan Lalata Kayan Kamfen Abokan Hamayyarsu Gabanin Zaɓen 2027
Ya bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kan jama’a da Cibiyar Northern Reform Organization ta shirya, domin tattauna hanyoyin ƙara wayar da kan masu zaɓe da ƙarfafa shigar al’umma cikin harkokin zaɓe.
Masanin ya ce ya kamata masu zaɓe su fahimci muhimmancin ƙuri’arsu, su kuma yi amfani da ita cikin hikima, ba tare da barin tasirin jam’iyya ko wasu mutane ya rinjayi shawarar da za su yanke ba.
Ya ƙara da cewa ya kamata ’yan ƙasa su riƙa nazarin halayen ’yan takara, manufofinsu da irin ayyukan da suka gudanar kafin su yanke shawarar wanda za su zaɓa.
Farfesa Fagge ya kuma nuna cewa jam’iyyun siyasa na da babban nauyi wajen ilmantar da al’umma kan muhimmancin zaɓe, sai dai akwai buƙatar su ƙara himma wajen gudanar da wannan aiki.
Ya ce wayar da kan masu zaɓe ba aikin hukumar zaɓe kaɗai ba ne, domin kafofin yaɗa labarai, ƙungiyoyin fararen hula, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki duk suna da rawar da za su taka.
Ya jaddada cewa fahimtar al’umma game da ikon da suke da shi na zaɓen shugabanni na da muhimmanci wajen tabbatar da zaɓe mai inganci da kuma inganta tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya.
-
News3 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News1 day ago
Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Shirin Farfaɗo Da Kamfanin Jirgin Saman Nigeria Air
-
News4 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
