Connect with us

News

KANO: Jami’an Ƴansanda Sun Kama Ta’ambo Wanda Ake Zargi Da Jagorantar Daba Da Satar Waya A Rimin Kebe Da Kewaye

Published

on

IMG 20261105 233231 249
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani da ake zargi da daba, Umar Usman, wanda aka fi sani da ‘Ta’ambo’, bisa zargin daba, ƙwacen waya da kuma kai hari ga jami’an tsaro a yankin Rimin Kebe da kewaye.

Usman, mai shekaru 25, an kama shi ta hannun jami’an sashen ‘yan sandan Zango bayan makonni na sa ido da tattara bayanan sirri.

Wani Matashi Ya Soka Wa Maƙwabcinsa Wuƙa Har Lahira A Kan Tsire

‘Yan sandan sun ce ana zargin shi da ta’addancin mazauna Rimin Kebe, Ramin Research Area da kuma unguwar Galula.

Wanda yake hannun ‘yan sanda, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kama sauran abokan aikata laifukan da ake zargin suna tare da shi, domin ƙwato kayayyakin da aka sata da kuma makaman da suke amfani da su.

A ƙarshe, ƴan sandan sun ce za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan an kammala bincike.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending