News
EFCC Ta Fara Binciken Ciyamomin Ƙananan Hukumomi 774

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta fara bincike cikin sirri akan shugabannnin ƙananan hukumomi 774 na sassan Nijeriya kan halin gudanarwa da kashe-kashen kuɗaɗen al’umma tun daga lokacin da aka ba su ‘yancin cin gashin kai.
Binciken, wanda daraktocin shiyyoyi ke jagoranta, na da nufin duba ko ciyamomin ƙananan hukumomin suna ƙoƙarin tsare gaskiya da adalci yayin sarrafa kuɗaɗen da aka ba su. Wani jami’in ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi ta jiha, wanda ya tabbatar da ci-gaban, ya shaida wa wakilinmu cewa jami’an EFCC na binciken baki ɗaya ciyamomin ƙananan hukumomin jihar.
INEC Ta Cire Sunayen Mutane Miliyan Daya Da Dubu Dari Shida Daga Kundin Masu Zabe
A cewarsa, EFCC na duba yadda ciyamomin suka gudanar da kuɗaɗen da aka ware wa ƙananan hukumominsu, ƙarfin ikonsu na gudanar da kuɗaɗen al’umma da kuma wane mataki ‘yancin cin gashin kai ya inganta lamuran hidimar al’umma. Majiyoyi daga EFCC sun ce ana bincike a baki ɗaya jihohin Nijeriya 36 har da Abuja, kuma ana aikin ne bisa sirri.
Wannan mataki na zuwa ne bayan sama da shekara biyu da Kotun Ƙoli ta tabbatar da dokar ‘yancin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi 774 na faɗin Nijeriya kuma ta haramta wa gwamnonin jihohi gudanar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin.
