News
Tsadar Abincin Kaji Ta Durƙusar Da Sana’ar Kiwo A Arewa Maso Yamma – Rahoto Tsadar Abincin Kaji Na Durƙusar Da Sana’ar Kiwon A jihohin Arewa — Rahoto

Wasu manoman kaji da masu kiwon dabbobi a jihohin Kebbi, Sokoto da Zamfara sun dakatar da sana’arsu sakamakon tsadar abincin dabbobi, wadda ke ƙara jefa harkar kiwo cikin mawuyacin hali.
Wani bincike da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya gudanar ya nuna cewa matsalar tsaro, wadda ta hana manoma zuwa gonakinsu, na daga cikin abubuwan da suka haddasa raguwar noman hatsi, musamman masara da waken soya da ake amfani da su wajen sarrafa abincin kaji da sauran dabbobi.
Jihar Kano Za Ta Karɓi Bakuncin Babban Taron Bunkasa Kiwon Kaji Na Arewacin Nijeriya
Wani likitan dabbobi a jihar Kebbi, Dakta Abubakar Umar-Bunza, ya ce tsadar abincin kaji ta tilasta wa wasu ƙananan masu kiwo rufe gonakinsu saboda rashin samun ribar da za ta ba su damar ci gaba da sana’ar.
Ya bayyana cewa buhun masara mai nauyin kilo 100 ya taɓa kai wa Naira 70,000, yayin da farashin buhun waken soya ya haura Naira 90,000.
A cewarsa, tsadar sufuri, takin zamani da sauyin farashin canjin kuɗi na daga cikin abubuwan da ke ƙara tsadar kayan da ake amfani da su wajen samar da abincin dabbobi.
A jihar Zamfara kuwa, shugaban Ƙungiyar Masu Kiwon Kaji ta Ƙasa reshen jihar, Alhaji Zayyanu Ahmad, ya ce buhun abincin kaji da a baya ake sayarwa kan Naira 9,000, yanzu ya koma tsakanin Naira 20,000 zuwa Naira 23,000.
Ya ce abincin kaji na cinye tsakanin kashi 70 zuwa 75 cikin 100 na kuɗin da ake kashewa wajen kiwo, lamarin da ke jefa masu sana’ar cikin asara, musamman ganin yadda ƙarfin sayen ƙwai da kaji ya ragu a tsakanin al’umma.
A wani ɓangare kuma, wasu masu kiwon dabbobi a jihar Sokoto sun ce tsadar abinci ta tilasta musu rage yawan dabbobin da suke kiwo, yayin da wasu suka sayar da su gaba ɗaya.
Ɗaya daga cikinsu, Safiyanu Musa, ya ce ya sayar da awaki kusan 15 saboda ya kasa ci gaba da ciyar da su sakamakon tsadar abincin dabbobi.
Masu kiwon sun yi kira ga gwamnati da ta kawo musu ɗauki ta hanyar rage kuɗin kayan da ake amfani da su wajen sarrafa abincin dabbobi, tare da ƙarfafa noman masara da waken soya.
Sun kuma buƙaci a samar da masana’antun sarrafa abincin dabbobi masu rahusa da kuma lamunin kuɗi cikin sauƙi domin taimaka wa masu kiwo su ci gaba da sana’arsu.
Sun yi gargaɗin cewa rashin ɗaukar matakan gaggawa na iya janyo durƙushewar ƙarin gonakin kiwo, wanda zai iya haifar da ƙarancin ƙwai da nama a kasuwanni tare da ƙara tsadar abinci mai gina jiki a Najeriya.
