Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta EFCC sun yi dirar-mikiya a kasuwar ‘yan canji da ke unguwar Wuse Zone 4 a Abuja da zimmar yaƙi da masu ɓoye kuɗaɗen ƙetare, a cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Rahotanni sun ce EFCC ta ɗauki matakin ne don zaƙulo ‘yan kasuwar da ke saya suna ɓoye kuɗaɗen ƙasar waje musamman dalar Amurka, abin da ya sa darajar kuɗin ƙasar na naira ke faɗuwa a kwanan nan.
Kotun majistre ta umarci matashi da ya share haraba bisa yunƙurin yin sata
Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa samamen ya biyo bayan shirin da suka daɗe suna yi ne, inda suka dinga sa ido kan ‘yan canjin da ake zargin suna sayen dalar don ɓoyewa da kuma fita da ita daga Najeriya.
EFCC ta tura jami’anta zuwa manyan filayen jirgin sama na ƙasa kamar a Kano da Legas da Fatakwal da zimmar kama masu yunƙurin fita da kuɗin, a cewar rahoton.
A jiya Alhamis ne darajar naira ta yi mummunar faɗuwar da ba ta taɓa yi ba, inda aka dinga canzar da dala ɗaya kan N705 a kasuwar bayan fage.
